An dakatad da zama a majalisar dattawa kan mutuwar Sanata Longjan

An dakatad da zama a majalisar dattawa kan mutuwar Sanata Longjan

Majalisar dattawan tarayya a ranar Talata ta dakatad da zama da dukkan ayyukanta domin makokin mutuwar marigayi Sanata Ignatius Longjan.

Sanata Longjan wanda ya wakilci Plateau ta kudu a majalisar ya mutu ne a asibitin kasar Turkiyya dake Abuja ranar Lahadi.

Shugaban masu rinjaye a majalisar, Sanata Yahaya Abdullahi, ya gabatar da hakan ne a zauren majalisa kuma shugaban marasa rinjaye, Sanata Eyinnaya Abaribe, ya amince da hakan.

Mataimakin shugaban majalisa, Ovie Omo-Agege, wanda ya jagoranci zaman majalisar yau ya sanar da cewa gobe za'a karrama marigayi Sanata Benjamin Uwajumogu, wanda ya mutu a Disamba, 2019.

Omo-Agege ya yi kira ga abokan aikinsa su sanya farin kaya ko baki gobe.

An dakatad da zama a majalisar dattawa kan mutuwar Sanata Longjan
An dakatad da zama a majalisar dattawa kan mutuwar Sanata Longjan
Asali: Facebook

A bangare guda, Fitaccen Lauya, Femi Falana SAN, ya yi kira ga ‘Yan Najeriya su bukaci a inganta harkar kiwon lafiya a karkashin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Femi Falana ya bayyana cewa bai dace shugaba Buhari ya rika zuwa asibitocin kasar waje domin samun kulawa ba, amma an bar ‘Yan Najeriya a asibitocin gida.

Lauyan wanda ya yi kaurin suna wajen kare hakkin Bil Adama a kasar, ya misalta asibotcin Najeriya a gwamnatin shugaban kasa Buhari da dakunan ajiye gawa.

Falana ya bayyana cewa a lokacin da Buhari ya ke mulkin Soji, ya daure Dr. Beko Ransome-Kuti, don kurum ya bukaci gwamnati ta inganta asibitocin da ke Najeriya.

Gawurtaccen Lauyan ya yi wannan jawabi ne wajen wata laccar musamman da wata kungiyar kare Bil Adama ta shirya domin tunawa da Marigayi Beko Ransome-Kuti.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel