Kashi 87% masu fama da talauci a Najeriya yan Arewa ne - Bankin Duniya

Kashi 87% masu fama da talauci a Najeriya yan Arewa ne - Bankin Duniya

Bayan jawabin mai martaba sarkin Kano, Bankin duniya ta saki rahoton cewa kimanin kashi 87 masu fama da talauci a Najeriya yan Arewacin kasar ne.

A rahoton da bankin ta saki, ta bayyana cewa yankin kudu maso kudu ce yankin da ta samu raguwan talauci tsakanin shekarar 2011 da 2016.

Yace: "Talauci a Arewacin Najeriya na karuwa musamman a yankin Arewa maso yammacin kasar."

"Kimanin rabin masu fama da talauci na Arewa maso yamma kuma kashi 87 na talakawan kasar na Arewacin Najeriya."

"Talauci a kudancin Najeriya kimanin kashi 12 ne. Yankin kudu maso kudu ce yanki mai karancin talauci tsakanin 2011 da 2016."

"Kashi 64 na dukkan talakawan Najeriya na zaune a karkara kuma kashi 52 na masu zama a karkara talakawa ne."

"Amma kashi 16 na talakawan Najeriya ne zaune a birane tsakanin 2011 da 2016."

Kashi 87% masu fama da talauci a Najeriya yan Arewa ne - Bankin Duniya
Kashi 87% masu fama da talauci a Najeriya yan Arewa ne - Bankin Duniya
Asali: Depositphotos

Mun kawo muku rahoton cewa kungiyar kiwon lafiyar duniya WHO ta bayyana Abuja, Kano, Legas, Cross River, Akwa Ibom, Port Harcourt, Enugu, Delta da Bayelsa matsayin jihohin da ya kamata a shirya matakan tsaro idan cutar Coronavirus ta bulla a Najeriya.

Babbar jami'ar WHO, Dhamari Naidoo, ta bayyana hakan ne a karshen makon da ya gabata a taron horar da yan jarida kan cutar Coronavirus.

Tace: "Kungiyar kiwon lafiyar duniya WHO ta bayyana Najeriya matsayin kasa mai mugun hadarin kamuwa da cutar saboda yawan sufuri tsakanin kasar Sin da Najeriya."

Ta ce WHO na aiki kan karfafa tsaro a iyakokin shiga Najeriya da kuma taimakawa wajen gano zafin jiki da fuskokin masu shigowa.

Dhamari Naidoo ta kara da cewa an sanar da dukkan kamfanonin jiragen sama su yi kyakkyawan lura da masu shigowa Najeriya daga Sin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel