Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da fasinjoji 9 a kan hanyar Abuja

Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da fasinjoji 9 a kan hanyar Abuja

Wasu miyagun yan bindiga sun tare babbar hanyar Lokoja zuwa Abuja inda suka yi awon gaba da mutane cikin daji, daga cikinsu har da wani matashi dan bautan kasa mai suna Samuel Adigun.

Rahoton jaridar Daily Trust ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a daidai kauyen Idu a ranar Alhamis da ta gabata, kamar yadda wani mazaunin ya tabbatar, inda yace yan bindigan suna sanye da kakin Sojoji ne, kuma dauke da muggan makamai.

KU KARANTA: Allah Ya kiyaye: Cutar ‘Corona Virus’ ta halaka fiye da mutane 900 a kasar Sin

Matashi dan bautan kasa, Samuel yana gudanar da aikin yi ma kasa hidima ne a Abaji na babban birnin tarayya Abuja, kuma yana kan hanyarsa ta komawa garin Lokoja daga Abaji ne lamarin ya rutsa da shi.

Majiyar ya bayyana cewa yan bindigan sun fito ne daga cikin daji, inda suka bude ma wata mota kirar Toyota wuta, suka samu tayoyinta, wanda hakan yasa dole direban motar ya tsaya, ba tare da bata lokaci ba suka yi awon gaba da Samuel da fasinjoji 8.

“Ina cikin rafi ina wanke babur a lokacin da na ji karar harbe harbe, nan da nan na kwanta a kasa, har sai bayan da miyagun suka hau tsakiyar titi suka kwashe fasinjojin motar sa’annan na tashi na tsere.” Inji shi.

Shi ma wani babban jami’in hukumar NYSC ya tabbatar da sace Samuel, kuma yace tuni sun fara magana da yan bindigan har ma an fara ciniki, inda yace suna sa ran za’a sakesu cikin yan kwanakin nan.

A wani labari kuma, fadar shugaban kasar Najeriya ta yi fatali da bayanan da kungiyar dattawan Arewacin Najeriya, Arewa Elders Forum fitar game da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda ta bayyana kungiyar a matsayin kungiyar mutum guda.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya ta ruwaito a ranar Lahadi, 9 ga watan Feburairu ne kungiyar ta fitar da wata sanarwa inda ta bayyana gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta gaza wajen shawo kan matsalar tsaro da talauci a Najeriya.

Kungiyar ta bakin shugabanta, Farfesa Ango Abdullahi ta bayyana cewa: “Talauci da matsalar tsaro sun kara ta’zzara a yankin Arewacin Najeriya a karkashin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel