Allah Ya kiyaye: Cutar ‘Corona Virus’ ta halaka fiye da mutane 900 a kasar Sin

Allah Ya kiyaye: Cutar ‘Corona Virus’ ta halaka fiye da mutane 900 a kasar Sin

Kididdigan alkalumma sun tabbatar da cutar Corona Virus ta kashe sama da mutane 900 a kasar Sin, watau China tun bayan bullatar watanni biyu da suka gabata, inji rahoton gidan talabijin na Channels.

Wadannan alkalumma sun tabbatar da cewa barnar da Corona Virus ta yi ya haura wanda cutar SARS ta yi a lokacin da ta zama annoba a tsakanin shekarar 2002 da 2003, koda yake dai kungiyar kiwon lafiya ta duniya, WHO, ta ce cutar da sauki yanzu.

KU KARANTA: Sanata Ndume ya fadi mawuyacin halin da Sojoji suka sanya mayakan Boko Haram

A shekarar 2002-2003 da cutar SARS ta barke, ta kashe mutane 774, amma biyo bayan samun karin mutane 91 da cutar Corona Virus ta kashe a lardin Hubei na kasar China a yan kwanakin nan, yasa Corona ta dara SARS wajen yin barna.

Kungiyar WHO ta bayyana cewa a kwanaki hudu da suka gabata an samu dan saukin cutar a yankin Hubei, amma ta yi gargadin akwai yiwuwar kara samun mace mace a sakamakon yaduwar cutar.

Akalla jama’an kasar Sin su 39,800 ne suka kamu da cutar, kuma ta samo asali ne a birnin Wuhan, babban birnin lardin Hubei inda jama’a suke yawan hada hadar kasuwanci, hakan ne yasa gwamnati ta garkame garin gaba daya.

Sai dai jama’an garuruwan da dokar ta bacin ya shafa sun bayyana damuwarsu game da tsananin dokar, sakamakon an bukaci kowa ya zauna a gida babu shiga babu fita, toh amma kuma babu abinci, babu kudi, don haka suke bukatar zuwa shaguna sayo abinci da bankuna don cirar kudi, gwamnati kuma ta hana.

A wani labari kuma, fadar shugaban kasar Najeriya ta yi fatali da bayanan da kungiyar dattawan Arewacin Najeriya, Arewa Elders Forum fitar game da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda ta bayyana kungiyar a matsayin kungiyar mutum guda.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya ta ruwaito a ranar Lahadi, 9 ga watan Feburairu ne kungiyar ta fitar da wata sanarwa inda ta bayyana gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta gaza wajen shawo kan matsalar tsaro da talauci a Najeriya.

Kungiyar ta bakin shugabanta, Farfesa Ango Abdullahi ta bayyana cewa: “Talauci da matsalar tsaro sun kara ta’zzara a yankin Arewacin Najeriya a karkashin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel