Badakalar N150bn: EFCC ta haramtawa tsohon gwamnan Abia da yaransa biyu fita daga Najeriya

Badakalar N150bn: EFCC ta haramtawa tsohon gwamnan Abia da yaransa biyu fita daga Najeriya

A cigaba da binciken da hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin zagon kasa EFCC ke gudanar kan tsohon gwamnan jihar Abia, wanda yake Sanata mai ci a yanzu, Theodore Orji, na zargin badakalar N150bn lokacin da ya mulki jihar, an kwashe littafin biza da fita daga kasar sa.

Hakazalika hukumar ta hada da na yaransa biyu, Chinendum Orji Eyinanya, wanda yake kakakin majalisar dokokin jihar Abia a yanzu, da Ogbonna Orji.

An haramta musu fita daga Najeriya har sai an kammala binciken da ake gudanarwa akansu.

A cewar EFCC, kwace fasfot dinsu ne na cikin sharrudan belin da aka baiwa gwamnan da yaransa biyu.

Mun kawo muku rahoton cewa EFCC) ta bankado yadda tsohon gwamnan jihar Abia, Theodore Orji, ya shafe tsawon shekaru takwas (8) yana wawurar miliyan N500 kowani daga asusun jihar lokacin da yake kan karagar mulki.

Cikin shekaru 8, ya yi rub da ciki da Bilyan N48 da sunan kudin samar da tsaro.

Badakalar N150bn: EFCC ta kwace fasfot din tsohon gwamnan Abia da yaransa biyu
Badakalar N150bn: EFCC ta kwace fasfot din tsohon gwamnan Abia da yaransa biyu
Asali: UGC

EFCC ta ce tsohon gwamnan ya fara kwasar kudin ne tun lokacin da yake rike da mukamin shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin Abia a lokacin mulkin tsohon gwamnan jihar, Orji Uzor Kalu, wanda aka yanke wa hukuncin dauri bayan samunsa da laifin tafka almundahana.

Hukumar ta fara binciken hada hadar kudade da tsohon gwamnan ke yi bayan ta karbi wani korafi da wata kungiya mai rajin yaki da cin hanci, 'Save Nigeria Group', ta aika mata a kansa.

A cikin takardar korafin, kungiyar ta yi zargin cewa dukkan kudaden da gwamnan ke fitar wa duk wata daga asusun jihar, suna tafiya ne wajen biyan bukatun kansa.

Kungiyar ta bayyana cewa N500m da gwamnan ke fitar wa duk wata basa daga cikin kudaden da jihar ke kashe wa a kan harkokin tsaron jihar.

Wata majiya ta bayyana cewa EFCC ta fadada bincikenta zuwa kan wasu 'yan uwa na jini ga tsohon gwamnan domin bankado rawar da suka taka a cikin badakalar da ya tafka.

EFCC ta bankado a kalla asusu 100 da ke da nasaba da Chinedum tare da gano wasu asusu fiye da 145 na 'yan uwan tsohon gwamnan da ya yi amfani da su wajen karkatar da biliyan N150.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel