Yan ta'adda sun kai farmaki hanyar Maiduguri-Damaturu, sun kashe 9

Yan ta'adda sun kai farmaki hanyar Maiduguri-Damaturu, sun kashe 9

Wasu yan ta'addan Boko Haram sun hallaka mutane tara yayinda sukayi garkuwa da fasinjoji da dama a hanyar Maiduguri-Damaturu a ranar Lahadi, 9 ga watan Febrairu, 2020.

Rahoton Daily Trust ya bayyana cewa an kai wannan hari ne misalin karfe 9:50 na daren Lahadi a karamar hukumar Konduga ta jihar Borno.

Bisa jawabin idanuwan shaida, yan ta'addan sun kona motoci 17 da dukiyoyin miliyoyin naira.

Wani mazauni, Ba'na Auni, wanda ya tsallake rijiya da baya yace yan ta'addan sun farwa fasinjojin da suka tsaya a garin Auno sakamakon kulle titin shiga Maiduguri da karfe 6 na yamma.

Yace: "Sun zo misalin karfe 9:50 na daren Lahadi kuma suka fara harbin mai uwa da wabi har muka arce cikin daji."

"Amma da muka dawo garin Auno da safen nan, mun samu an kashe fasinjoji tara amma mun gaza gane fuskokin biyar daga cikinsu ba saboda konewar da sukayi ,".

DUBA NAN: Ba mu da kudin aiwatar da ayyukanmu - Yan majalisar wakilai sun koka

Wani mazaunin, Modu Babagana, ya bayyana cewa an yi garkuwa da mata da dama kuma an kona gidajen mutane.

Hakazalika ya ce sun kona motoci takwas jibge da kayan abinci .

Modu yace: "Sun yi awon gaba da motoci kirar Hummer Bus, Golf, J5 dauke da mata. Kana sun yi sata a gidaje da shagunan mutane kafin suka banka musu wuta."

A bangare guda, a jiya Lahadin, gwamnatin jihar Borno ta bude titin Maiduguri zuwa Dikwa, bayan shekaru biyar da rufeta sakamakon rikicin Boko Haram da ya addabi Arewa maso gabashin Najeriya, musamman jihar Borno.

NAN ta ruwaito cewa an rufe hanyar mai tsawon kilomita 86 ne a shekarar 2015 yayinda rikicin Boko Haram yayi kamari.

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, tare da tiyata kwamandan , Operation Lafiya Dole, Manjo Janar Olusegun Adeniyi da GOC na 7 Div, , Operation Lafiya Dole, Birgediya Janar, Abdul Khalifa , suka bude hanyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel