Ba mu da kudin aiwatar da ayyukanmu - Yan majalisar wakilai sun koka

Ba mu da kudin aiwatar da ayyukanmu - Yan majalisar wakilai sun koka

- Majalisar Wakilan tarayya ta kaiwa yan Najeriya kukan rashin kudi

- Shugaban kwamitin yada labaran majalisar ya ce ayyuka sun yi musu yawa amma babu kudi

Yan Majalisar wakilan tarayya sun bayyana cewa ba su da isasshen kudin gudanar da ayyukansu na majalisa.

Mai magana da yawun majalisar, Benjamin Kalu, ya bayyana hakan ne a Abuja yayinda yake hira da manema labarai kan kukan da wasu kwamitocin majalisar keyi.

Har yanzu, majalisar dokokin tarayya basu bayyanawa yan Najeriya abinda ke kunshe cikin kasafin kudinsu na N128bn na 2020 ba.

Da wannan kasafin kudin za'a biya kudin albashin sanatoci 109 da yan majalisu 360, dukkan hadimansu, ma'aikatan hukumar majalisar dokokin, ma'aikatan kwalejin ilimin demokradiyya da ayyukan majalisa NILDS.

Ba mu da kudin aiwatar da ayyukanmu - Yan majalisar wakilai sun koka
Ba mu da kudin aiwatar da ayyukanmu - Yan majalisar wakilai sun koka
Asali: Facebook

KU KARANTA: Bayan shekaru 5, an bude hanyar Maiduguri-Dikwa

Benjamin Kalu yace: "Mun fito fili da wannan bayani ne saboda mutane su san abinda mukeyi a majalisar wakilan tarayya. Ayyukan na da yawa amma kudaden sun yi kadan.

"Mutane da dama ba za'a su so jin hakan ba, amma wannan ne gaskiyar magana."

"Ba ayyukan mazabu muke magana ba, amma ayyukan samar da dokoki da lura da sauransu."

"Kudin ba zai isa ba. Saboda haka, idan wani kwamiti yayi korafi, ba wai dan ba'a son sakin kudi bane. Kawai ana kokarin tattalin kudin da ake dashi ne."

Mun kawo muku rahoton cewa cewa Sanata Ignicious Longjan mai wakiltar mazabar Plateau ta kudu a majalisar dattawa, ya rigamu gidan gaskiya.

Sanatan ya mutu ne a wani Asibitin kasar Turkiyya Mai maga da yawun Sanatan, Mr Wulime Goyit, ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a garin Jos.

Gabanin zama Sanata, Ignacious Longjan, ya kasance mataimakin gwamnan jihar Plateau karkashin tsohon gwamna, Jonah Jang.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel