Rikicin PDP: Secondus zai bayyana a gaban kotu

Rikicin PDP: Secondus zai bayyana a gaban kotu

Shugaban jam'iyyar PDP ta kasa, Prince Uche Secondus zai bayyana a gaban wata babbar kotun jihar Legas a yau Litinin. Zai bayyana ne saboda karar da aka shigar mai kalubalantar bayyanar Deji Doherty a matsayin shugaban jam'iyyar a jihar Legas.

Mai shari'a Taofikat Oyekan Abdullahi ta babbar kotun ce ta bukaci bayyanar Secondus da kuma Sanata Ben Obi wanda ya jagoranci kwamitin, a gaban kotun.

Mai shari'ar ta bukaci Secondus da Sanata Obi da su zo su yi bayanin dalilin da yasa ba za a jefa su gidan gyaran hali ba saboda take dokar kotun da suka yi inda ta ce a dakatar da zabe.

A ranar 12 ga watan Nuwamba na 2019 ne kotun ta ba wa jam'iyyun umarnin su zauna lafiya kuma a bar zababbun shugabannin a kujerunsu tare da watsi da zabe na musamman da suke shiryawa don samar da shugabannin sabbi.

Rikicin PDP: Secondus zai bayyana a gaban kotu
Rikicin PDP: Secondus zai bayyana a gaban kotu
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Ina busar iska zan saki bidiyon kaina tsirara - Nafisa Abdullahi

Mai shari'a Oyekan Abdullahi ta nuna rashin jin dadinta da yadda PDP din jihar Legas ta yi zaben na musamman duk da kuwa ta san lamarin na gaban kotu kuma ba a kammala shari'ar ba.

Shugaban jam'iyyar da za a sauke tare da wasu mutane bakwai sun tunkari kotun da bukatar cewa a dakatar da jam'iyyar da 'ya'yanta daga yin zaben da suka shirya na ranar 13 ga watan Nuwamba. Lamarin da kotun ta yarje.

Sauran wadanda suka bukaci hakan tare da Dominic sun hada da Babatunde Agbaje, Adeniyi Funsho Pakanu, Kehinde Oshinowo, Ademola Badejo, Alhaja Fatai Ajisefunmi, Bidemi Akojenu da Chief Taiwo Kuye.

Wadanda ake karar kuwa sun hada da jam'iyyar PDP, Sanata Ben Obi, Biodun Olujimi, Jarigbe Agom Jarigbe, Danladi Baidu Tijo, Injiniya Ahmed M. Mukhtar da kuma INEC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel