Ba ka da kowa a Arewa, daga kai sai kai – Shugaba Buhari ga Farfesa Ango Abdullahi

Ba ka da kowa a Arewa, daga kai sai kai – Shugaba Buhari ga Farfesa Ango Abdullahi

Fadar shugaban kasar Najeriya ta yi fatali da bayanan da kungiyar dattawan Arewacin Najeriya, Arewa Elders Forum fitar game da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda ta bayyana kungiyar a matsayin kungiyar mutum guda.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya ta ruwaito a ranar Lahadi, 9 ga watan Feburairu ne kungiyar ta fitar da wata sanarwa inda ta bayyana gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta gaza wajen shawo kan matsalar tsaro da talauci a Najeriya.

KU KARANTA: Hotuna: Musulman kasar Japan sun samar da Masallacin tafi da gidanka

Kungiyar ta bakin shugabanta, Farfesa Ango Abdullahi ta bayyana cewa: “Talauci da matsalar tsaro sun kara ta’zzara a yankin Arewacin Najeriya a karkashin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari.”

Sai dai mai magana da yawun shugaban kasa Femi Adesina ya mayar ma NEF da raddi ba tare da bata lokaci ba, inda ya bayyana cewa ba wannan bane karo na farko da kungiyar take nuna kiyayya ga shugaba Buhari ba.

“A ranar Lahadi Farfesa Ango Abdullahi ya rattafa hannu kan wata doguwar sanarwa game da abubuwa da dama da suka shafi Arewa da ma kasar gaba daya, kai idan ka ji an ce kungiyar dattawan Arewa za ka dauka da gaske ta kunshi dattawa ne da gaske.

“Amma gaskiyar maganar ita ce kungiyar NEF ita ce Ango Abdullahi, kuma Ango Abdullahi shi ne NEF, kungiya ce da bata mambobi, kuma shugabanta tamkar kwamandan yaki ne mai mukamin janar amma ba shi da Sojoji.

“Haka ya yi kafin zaben 2019, inda yace wai NEF ba ta goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari, akwai dan takarar da yake so, amma Buhari ya hadasu gaba daya ya doke, don haka shure shure kawai NEF take yi saboda Buhari aikin tabbatar da daidaiton kasar ya sanya a gaba, kuma yan Najeriya sun sani, don haka basu bukatar wata damisar takarda ta fada musu wani abu.” Inji shi.

A wani labari kuma, Shugaban kwamitin majalisar dattawan Najeriya mai kula da rundunar Sojan kasa, Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa a yanzu dakarun rundunar Sojan kasa suna bin mayakan yan ta’addan Boko Haram har zuwa sansanoninsu domin gamawa dasu.

Ndume ya bayyana haka ne yayin da yake tattaunawa da manema labaru a babban birnin tarayya Abuja a ranar asabar, inda yace Sojojin sun samu kwarin gwiwa ne biyo bayan umarnin da rundunar Sojan kasa ta bayar na su dinga kaddamar da hare hare a kan yan ta’addan ba sai sun jirasu ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel