An tsinci gangan jikin mutum babu kai a Delta

An tsinci gangan jikin mutum babu kai a Delta

Hankulan mutane ya tashi a ranar Asabar bayan an tsinci gangan jikin wani mutum da aka datse wai kai a Nnebisi Road, Asaba a jihar Delta.

Sahara Reporters ta ruwaito cewa an kuma gano cewa an cire wasu sassan na jikin mutumin masu muhimmaci kafin daga bisani aka jefar da gawar.

Wani wanda ya gane wa idanunsa lamarin ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa, "Mun ga mutumin a daren ranar Juma'a yana yanayi kamar wanda ya sha wasu abubuwan maye. Amma dai dukkan sassan jikinsa suna nan lafiya.

An tsinci gangan jikin mutum babu kai a Delta
An tsinci gangan jikin mutum babu kai a Delta
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Matar aure ta lakada wa mijin ta duka domin ya gasa yi mata ciki

"Amma a safiyar ranar Asabar, sai muka tsinci gawarsa babu kai kuma an cire wasu sassa na jikinsa. Wannan abin ya bamu tsoro da mamaki. Irin wannan bai taba faruwa ba a wannan unguwar hakan yasa kowa yana cikin tsoro da fargaba."

Da aka tuntube shi domin samun karin bayani a kan lamarin, Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan Delta, Onome Onowvakpoyeya, ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda ya ce tuni rundunar ta kaddamar da bincike domin gano wanda ya aikata kisar a kuma gurfanar da shi gaban kuliya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel