Ansaru: Wani dan sanda cikin wadanda suka kai sumame a Kaduna ya sake mutuwa

Ansaru: Wani dan sanda cikin wadanda suka kai sumame a Kaduna ya sake mutuwa

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce daya daga cikin dakarun ta da suka kai sumame sansanin 'yan kungiyar tayar da kayan baya na Ansaru a Kaduna ya rasu.

AbdulMajeed Ali, mataimakin sufeta janar na 'yan sanda (sashin ayyuka), ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ziyarci 'yan sandan da suka samu rauni sakamakon sumamen na ranar Juma'a a Kaduna.

Ya ce jami'in dan sandan mai suna Idris ya mutu ne a ranar Juma'a sakamakon raunin da ya samu yayin sumamen.

Daya daga cikin 'yan sandan da suka kai sumame a Kaduna ya sake mutuwa
Daya daga cikin 'yan sandan da suka kai sumame a Kaduna ya sake mutuwa
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Matar aure ta lakada wa mijin ta duka domin ya gasa yi mata ciki

Idris ne dan sanda na biyu da ya mutu sakamakon sumamen. Dan sandan da aka sanar da mutuwarsa da farko sunansa Muhammed Abubakar.

Jami'an 'yan sanda 13 ne suka jikkata yayin sumamen da 'yan sandan suka kashe 'yan kungiyar tayar da kayan bayan 250 a cewar mai magana da yawun rundunar 'yan sanda Frank Mba.

Mba ya ce wadanda aka kashe sun hada da Haruna Basullube "daya daga cikin gawurattun masu garkuwa da mutane da ake nema ruwa a jallo" da kuma wani kwamandan masu tayar da kayan baya mai suna Bashir Leta."S

Rundunar 'yan sandan ta ce za ta cigaba da yakar masu tayar da kayan bayan, kazalika, ta gayyaci tawaga da musamman na masu binciken laifuka domin zurfafa bincike kan ayyukan kungiyar ta Ansaru da wadanda ke tallafa musu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel