Sunaye: Chiyamomi 8 na APC sun koma PDP a Zamfara

Sunaye: Chiyamomi 8 na APC sun koma PDP a Zamfara

Shugabannin kananan hukumomi takwas ne wadanda aka zaba karkashin jam'iyyar APC suka koma jam'iyyar PDP a yau Asabar.

Shugabannin kananan hukumomin da suka sauya shekar sun hada da: Alhaji Muhammadu Umar, shugaban karamar hukumar Birnin Magaji; Alhajj Salisu Isah Dangulbi, shugaban karamar hukumar Maru; Alhaji Nasiru Zarumi Masamar mudi, shugaban karamar hukumar Bukkuyum; Alhaji Ahmed Balarabe Anka, shugaban karamar hukumar Anka.

Sauran sun hada da shugaban karamar hukumar Kauran Namoda, Alhaji Lawali Abdullahi; Alhaji Shehu Muhammad Faru, shugaban karamar hukumar Maradun; Alhaji Abdulaziz Ahmed Nahuche, shugaban karamar hukumar Bungudu; Alhaji Aminu Mudi Tsafe, shugaban karamar hukumar Tsafe.

Shugabannin kananan hukumomin sun sauya sheka ne jim kadan bayan sunyi taro da Gwamna Bello Muhammad, Matawallen Maradun a jihar Sokoto, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Bidiyon tsiraicin wani Sanata: Kowa nayi, wasu sun fi wasu wayau - Sanata mai jaje

Alhaji Balarabe Anka ne ya sanar da manema labarai bayan taron da suka yi gwamnan. Ya ce sun yanke shawarar komawa PDP din ne sakamakon salon shugabancin Gwamna Matawalle da kuma yadda ya dawo da zaman lafiya a jihar cikin kankanin lokaci.

Alhaji Anka ya jaddada cewa, an samu daidaituwar siyasa, hadin kai da zaman lafiya a yayin da ya cika kwanaki 100. Hakan yana nufin kwarewar Matawalle shugabanci.

Shugabannin kananan hukumomin sun koma PDP din ne tare da magoya bayansu.

A yayin karbar shugabannin kananan hukumomin, Gwamna Matawalle ya mika godiya ga shugabannin tare da jinjina musu na hangen nesan da suka yi na komawa PDP a Zamfara.

Gwamna Matawalle yayi alkawarin mutunta su tare da tafiya tare da wadanda suka sauya sheka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel