Yanzu-yanzu: Bam ya tashi a gidan gwamnatin jihar Ekiti
Tashin hankali da hargitsi ya mamaye yankin Okesha na jihar Ekiti a yau ranar Asabar bayan da bam ya tashi a kusa da tsohon gidan gwamnatin jihar.
Jaridar The Cable ta gano cewa tashin bam din yayi sanadiyyar tarwatsewar wasu gine-gine a yankin. Kuma hakan ya shafi wani bangare na ma'aikatar masarautun jihar.
Tashin bam din ya kawo tarwatsewar wani bangare na ma'aikatar kudi da sauran gine-ginen da ke farfajiyar.

Asali: UGC
Amba Asuquo, kwamishinan 'yan sandan jihar ya hallara a inda abin ya faru. Ya ce an fara binciken farko don gano sanadin fashewar bam din a farfajiyar.
DUBA WANNAN: Faduwa zabe: Abdulmumin Kofa ya mayarwa majalisa dukiyoyinta
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng