Faduwa zabe: Abdulmumin Kofa ya mayarwa majalisa dukiyoyinta

Faduwa zabe: Abdulmumin Kofa ya mayarwa majalisa dukiyoyinta

Tsohon dan majalisar wakilai, Hon. Abdulmumin Jibrin, ya ce ya mika makomar siyasarsa zuwa ga Allah, amma kuma zai ci gaba da shiga siyasa. Jibrin ya sanar da manema labarai hakan ne bayan da ya mayarwa majalisar dattijai kadarorinsu da ke hannunshi. Ya mika su ne ga magatakardan majalisar wakilan Najeriya.

An soke zaben mazabar Kiru/Bebeji a kotun daukaka kara inda aka bada umarnin maimata zaben. Bayan maimaita zaben, Kofa ya sha mugun kaye a hannun Ali Datti-Yako, lamarin da yasa Kofa komawa gida daga majalisar wakilan.

Ya ce yana goyon bayan kowa ya shiga siyasa duk da kuwa hakan ba yana nufin dole sai mutum ya hau kujera bane.

Ya ce "Zaka iya zama dan jarida amma kuma kana goyon damokaradiyya. Zaka iya zama mutumin da ya dau kuri'arsa da muhimmanci."

Kano: Tsohon dan majalisa ya mayar da kadarorin ofishinsa
Kano: Tsohon dan majalisa ya mayar da kadarorin ofishinsa
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Abinda yasa rigingimu suka dabaibaye yankin arewa - Dogara

A yayin magana a kan abinda zai yi a siyasa nan gaba, tsohon dan majalisar ya ce ya bar komai ga Allah. Ya kara da cewa "akwai yuwuwar gaba tafi kyau. Kuma zan iya cewa na samu gogewa a zaman majalisar da nayi na shekaru 10.

"A shekarun da suka gabata, na rike manyan mukamai a majalisar. Na dau shekaru 10 ba tare da an zargeni da satar komai na majalisar ba. Ba a taba zargina da rashawa ba ko kuma rashin sanin aikina. Ina godiya ga Ubangiji".

A kan ko akwai abinda za a yi masa na kyautatawa saboda matsayin da ya rike a majalisar, Jibrin ya ce aikin mutane ne yayi kuma don su yayi.

"Bana bukatar komai kuma ban gaji da bautawa kasata ba. Ba zan gajiya ba wajen bauta mata a duk lokacin da hakan ya taso," ya ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel