Matar aure ta lakada wa mijin ta duka domin ya gasa yi mata ciki

Matar aure ta lakada wa mijin ta duka domin ya gasa yi mata ciki

An gurfanar da da wata matar aure mai shekaru 32, Chinwendu Chita a kotun Majistare a kan zargin dukan mijinta, Okechukwu Chita da wata 'yar sanda a gidansu da ke Alhaji Agbeke Street, Ago Palace a unguwar Okota a Legas.

Ana zargin matar da yi wa mijin duka saboda wai bai mayar da hankali a aurensu ba ya yi wa matarsa ciki wadda hakan yasa ya tsere daga gida ya ke kuma tsoro koma wa.

Chinwendu wacce ta fara dukan mijinta tun a 2018 ta tsananta dukkan bayan 'yan sanda sun shiga tsakani.

Matar aure ta lakada wa mijin ta duka domin ya kasa yi mata ciki
Matar aure ta lakada wa mijin ta duka domin ya kasa yi mata ciki
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Soja ya kashe dan sanda a filin daga saboda budurwa

An ce wacce aka yi karar da ci zarafin mijinta ta hanyar kulle shi a gidansu a ranar 22 ga watan Disamban 2019. Ta kuma yi amfani da cokalin suya ta fasa masa kai kafin ta tilasta shi ya ba ta N650,000 ko kuma ta kashe shi.

Chinwendu ta cigaba da dukan mijinta duk da gargadin da 'yan sanda su ka yi mata, an kuma ce ta doki wata 'yar sanda mai matayin saja Ojooniyan Omonike da DPO na caji ofis din Ago ya aika domin ta gayyace ta zuwa caji ofis.

PM Express ta ruwaito cewa matar da musanta dukkan zargin da ake mata bayan an gurfanar da ita a gaban Majistare na kotun Ejigbo Mista T.O. Shomade.

Shomade ya saka ranar da za a bawa 'yan sanda damar gabatar da hujojji a kan zargin da suka yi wa matan kuma ya bayar da ita beli a kan kudi N700,000.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel