2023: Cancanta za mu duba ba yanki ba wurin zaben dan takarar shugaban kasa - Sule Lamido

2023: Cancanta za mu duba ba yanki ba wurin zaben dan takarar shugaban kasa - Sule Lamido

Alhaji Sule Lamido, mai shekaru 71 yana daya daga mambobin jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) tun kafuwarta a 1998. Ya yi gwamna a jihar Jigawa daga 2007 zuwa 2015 kuma daga bisani ya yi ministan harkokin kasashen waje karkashin mulkin Shugab Olusegun Obasanjo.

Lamido ya hallarci taron tattaunawa na shekara-shekara da Daily Trust ta shirya inda ya yi magana a kan batutuwa da suka shafi demokradiyya a Najeriya, salon mulkin shugaba Muhammadu Buhari da sauransu.

An tambayi Lamido ka yana da niyyar takarar shugaban kasa a 2023 duba da cewa akwai fostocinsa da ke yawa a kafar Facebook inda ya bayar da masa kamar haka.

2023: Cancanta za mu duba ba yanki ba wurin zaben dan takarar shugaban kasa - Sule Lamido
2023: Cancanta za mu duba ba yanki ba wurin zaben dan takarar shugaban kasa - Sule Lamido
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Matar aure ta lakada wa mijin ta duka domin ya gasa yi mata ciki

"Ka ga, idan wani ya ce yana son ka zama gwamna, shin za ka ce ba ka so? Maganar gaskiya. Ka san mene abinda ake kira mulki? Na yi farin cikin cewa duk da yunkurin da aka yi na bata min suna wasu har yanzu ba su cire tsammani a kai na ba."

Da aka bijiro masa da batun tsarin karba-karba na jam'iyyar PDP wurin tsayar da dan takarar shugaban kasa da yadda hakan za ta shafi yiwuwar tsayarsa a 2023, Lamido ya kada baki ya ce:

"Bari in yi maka bayani, an kirkiro tsarin karba-karba ne a saboda Najeriya tana cikin wani mawuyacin hali da ya zama dole mu warware shi. Saboda haka mun bullo da hanyar da za mu sanyaya wa wani yanki zuciya shi yasa muka ce yanki na a, b, c, d. Za mu hana ka tikitin duk da cewa kana da ikon nema saboda dai a samu zaman lafiya da sulhu a jam'iyyar. Saboda haka an kirkiri karba-karba ne domin a ceto Najeriya, idan muna ganin mun tsira ya kamata mutane su fara neman mutumin da ya fi cancanta a matsayin shugaban Najeriya."

Da aka tambaye shi ko yana son ayi watsi da tsarin na kama-kama, Lamido ya ce shi duk wanda ya fi cancanta shi zai so ya zama shugaban Najeriya. Batu ne na mutunci, kima, dattaku da samar da tsaro, duk wanda zai iya tsare Najeriya shi ya kamata a zaba.

Ya kara da cewa demokradiyya ba kurkuku bace, tsari ce ta warware matsalolin mutane kuma wanda zai hada kan 'yan Najeriya ba tare da la'akari da addini ko kabilanci ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel