An yi karar diyar Buhari a kotu saboda amfani da jirgin shugaban kasa

An yi karar diyar Buhari a kotu saboda amfani da jirgin shugaban kasa

Wani lauya mazaunin Abuja, Mista Oluwatosin Ojaoma ya yi karar diyar shugaban kasa Muhammadu Buhari saboda ikirarin da ya yi na cewa ta yi amfani da jirgin shugaban kasa ba bisa ka'ida ba a yayin da ta tafi jihar Bauchi ranar 10 ga watan Janairu.

Saturday Punch ta gano kwafin takardun karar da lauyan ya shigar a babban kotun tarayya da ke Abuja a ranar 6 ga watan Fabrairu.

Hanan Buhari ce kadai aka yi karar ta a takardan mai lamba CV/1023/2020.

Wanda ya yi karar ya bukaci kotu ta umurci Hanan ta biya kudin man jirgin saman da kuma kudaden zirga-zirga a cikin asusun haraji na gwamnatin tarayya.

Ojaomo ya kuma bukaci kotun ta sanar da fili cewa ita Hanan din ba ta da ikon amfani da jirgin Shugaban kasa da aka samar saboda shugaban kasar da wasu manyan jamian gwamnati saboda gudanar da ayyuka da suka shafi ofisoshinsu.

Lauya ya maka diyar Buhari a kotu saboda amfani da jirgin shugaban kasa
Lauya ya maka diyar Buhari a kotu saboda amfani da jirgin shugaban kasa
Asali: Facebook

Ya kuma bukaci kotun ta bayar da oda na dindindin da zai hana wacce aka yi karar sake yin amfani da jirgin shugaban kasar domin bukatar kanta duba da cewa ita ba ma'aikaciyar gwamnati bane kamar yadda ta yi yayin zuwa Bauchi.

DUBA WANNAN: Matsala ce mai nasaba da tsarin kundin mulki - Ganduje ya yi magana a kan Sarki Sanusi II

Ya kuma bukaci kotun ta tursasa ta biyan kudin da ya kashe a kotun da ya tasanmu Naira miliyan 2.

Ojaomo ya kuma ce dalilin da yasa 'yan Najeriya suka zabi Shugaba Muhammadu Buhari shine domin ya yi wa 'yan Najeriya alkawarin cewa zai yaki cin hanci da rashawa har sai ya ga bayan shi kuma zai rage kashe kudaden gwamnati ya tabbatar an yi amfani da su domin yi wa 'yan Najeriya aiki.

Ya yi ikirarin cewa an kashe makuden kudi yayin tafiyar da Hanan ta yi zuwa Bauchi kuma ya ce ma'aikatar kudi ne za ta fi sanin ainihin abinda aka kashe.

Da aka tuntube shi a ranar Juma'a, Ojaomo ya ce bai riga ya mika wa diyar shugaban kasar takardan karar ba.

Ya ce, "Za mu yi kokarin ba ta takardun hannu da hannu amma idan hakan bai yi wu ba za mu bukaci kotu ta bamu izinin mika mata takardun ta wasu hanyoyin."

Rahotanni sun bayyana cewa diyar shugaban kasar ta tafi Bauchi ne domin amsa gayyatar da Sarkin Bauchi, Rilwani Adamu ya yi mata a matsayin bakuwa na musamman yayin bikin durbar da ya shirya.

Sai dai mai magana da yawun shugaban kasa Garba Shehu ya kare ta inda ya ce an bi dukkan dokokin da suka dace kafin ta yi amfani da jirgin na shugaban kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel