Kotun koli ta hana iyalan Abacha izinin taba kudadensa da ke kasashen waje

Kotun koli ta hana iyalan Abacha izinin taba kudadensa da ke kasashen waje

Kotun koli a ranar Juma'a 7 ga watan Fabrairu ta yi watsi da bukatar da iyalan tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Sani Abacha suka shigar na neman a basu izinin ciro kudade a wasu asusun ajiyar bakunansa a Burtaniya, Switzerland, Jersey, Liechenstein da Luxembourg.

Tun a shekarar 1999 ne gwamnatin Najeriya ta hana iyalan marigayin damar taba kudaden da ke asusun ajiyar cikin wata wasika da ministan Shari'a ne wannan lokacin Kanu Agabi (SAN) ya rubuta.

Da suke yanke hukuncin, alkalan biyar na kotun koli karkashin jagorancin Chima Nweze sun ce lokaci ya kure da iyalan marigayi Abacha za su iya yin korafi a kan matakin da gwamnatin tarayyar ta dauka tun a 1999.

Kotun na koli ta daukaka hukuncin da babban kotun tarayya na Kano da kotun daukaka kara na jihar Kaduna suka yanke kan batun.

Kotun koli ta hana iyalan Abacha taba kudadensa da ke kasashen ketare
Kotun koli ta hana iyalan Abacha taba kudadensa da ke kasashen ketare
Asali: Getty Images

DUBA WANNAN: Matsala ce mai nasaba da tsarin kundin mulki - Ganduje ya yi magana a kan Sarki Sanusi II

Mai shari'a Amina Augie wacce ta karanto hukuncin a madadin Mai shari'a Nweze da bai samu halartan zaman kotun na ranar ba ta ce

"Duk da irin bayyanan da wadanda suka shigar da karar su kayi da hujjojin da suka gabatar, ba ta bata lokaci ba wurin jadada hukuncin da kananan kotunan suka yanke.

"Kazalika, ina bayar da umurnin watsi da daukaka karar. Na kuma sake jadada hukuncin da kananan kotunan suka yi. Na yi watsi da daukaka karar."

An rufe asusun ajiyar bankunan ne a kasashen wajen sakamakon yarjejeniya da gwamnatin Najeriya ta yi da na kasashen ketaren lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo a 1999.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel