Yanzu-yanzu: Buhari ya dira Addis Ababa, kasar Habasha (Hotuna)

Yanzu-yanzu: Buhari ya dira Addis Ababa, kasar Habasha (Hotuna)

Shugaba Muhammadu Buhari ya dira birnin Addis Ababa, babbar birnin kasar Habasha kuma ya samu kyakkyawan tarba daga wajen Firam Minista Aby Ahmad a ranar Juma'a, 7 ga Febrairu, 2020.

Buhari ya tafi Habasha ne domin halartan taron gangamin shugabannin kasashen nahiyar Afrika karo na 33.

Fadar shugaban kasar ta bada jerin abubuwan da za su faru a can kasar Ethiopia.

Takardar ta ce, "Shugaban kasar zai halarci taron kungiyar shugabannin kasashe da gwamnatoci karo na 29. Zai ci gaba inda za a yi taron NEPAD karo na 27 tare da taron majalisar kashi na 33. A wannan taron ne shugaban kasa zai yi jawabi a kan tsaro. Gwamnatin Najeriya tare da hadin guiwar ta kasar Uganda da Norway ne suka dau wannan nauyin."

"Shugaban kasa Buhari da wakilai daga Najeriya za su shiga taron kasashe kan zaman lafiya, tsaro, yaki da ta'addanci, habakar tattalin arziki, yaki da rashawa da kuma karbo tattalin arzikin da aka handame." takardar ta kara da cewa.

Buhari zai yi taron tattaunawa a kan tattalin arziki tsakaninsa da sauran shugabannin kasar.

Bayan nan kuwa, Shugaban kasa Buhari zai karasa zuwa ziyarar kasar Ethiopia a ranar 11 ga watan Fabrairu, don amsa gayyatar da Firayim minista Dr Abiy Ahmed yayi masa.

Shugaban kasar zai dawo Najeriya ne a ranar 12 ga watan Fabrairu 2020.

Ya yi tafiyar ne tare da Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo da Ben Ayade na jihar Cross River.

Shugaban kwamitin majalisar kasar nan a kan harkokin waje, Sanata Adamu Mohammed-Bulkachuwa da kuma Yusuf Baba zasu shiga cikin tawagar shugaban kasar.

Sauran sun hada da Geoffrey Onyeama, Hadi Sirika, Otunba Niyi Adebayo, Manjo Janar Bashir Magashi, Lai Mohammed da kuma Gloria Akobudu.

Yanzu-yanzu: Buhari ya dira Addis Ababa, kasar Habasha (Hotuna)
Yanzu-yanzu: Buhari ya dira Addis Ababa, kasar Habasha (Hotuna)
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel