Hotuna: Musulman kasar Japan sun samar da Masallacin tafi da gidanka

Hotuna: Musulman kasar Japan sun samar da Masallacin tafi da gidanka

Musulmai a kasar Japan sun kirkiro wani sabon salon ginin Masallaci, wanda suke yi ma lakabi da Masallacin tafi da gidanka, wanda aka kera shi tamkar motar a kori kura, amma da zarar ka shiga sai ka tarar ashe masallaci ne.

Kamfanin jaridar Aminiya ta ruwaito a yanzu haka wannan Masallaci ya yawaita a birnin Tokyo, babban birnin kasar Japan, kuma yana kewayawa unguwanni da manyan titunan birnin domin baiwa Musulmai daman gudanar da ibadar Sallah.

KU KARANTA: Taskar Kannywood: Gwamnatin Ganduje ta bude ma Sani Danja kamfaninsa da ta garkame

Hotuna: Musulman kasar Japan sun samar da Masallacin tafi da gidanka
Hotuna: Musulman kasar Japan sun samar da Masallacin tafi da gidanka
Asali: Facebook

Dalilin da ya sabbaba kirkiro wannan masallaci shi ne domin samar da dama ta tafi da gidanka ga Musulmi domin su samu tsaftatacce kuma ingantaccen wurin da zasu gudanar da ibada a yayin da ake gudanar da gasar wasannin Olympics a birnin Tokyo a 2020.

Shi dai wannan masallaci na tafi da gidanka yana da fadin murabba’in mita 48, kuma an gina shi ne a bayan mota, ta yadda za a iya bude shi bayan motar ta tsaya, a shiga a gudanar da sallah a kan kafet dake shimfide.

A ranar Laraba, 5 ga watan Feburairu ne masu shirya gasar Olympics a birnin Tokyo na shekarar 2020 suka bayyana cewa suna duba duk hanyoyin da za su samar wa kowane addini damar yin ibadarsa yadda ya kamata a lokacin gasar.

Hotuna: Musulman kasar Japan sun samar da Masallacin tafi da gidanka
Hotuna: Musulman kasar Japan sun samar da Masallacin tafi da gidanka
Asali: Facebook

A cewar jami’an, akwai masallatai 105 a duk fadin kasar Japan; koda yake, da dama cikinsu kanana ne kuma suna wajen birnin Tokyo ne wanda hakan zai sanya Musulmi cikin matsi wajen yin salloli biyar a rana.

A wani labari kuma, dakarun rundunar Sojan saman Najeriya sun tashi wasu sansanonin mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram, bangaren ISWAP a kauyen Kaza, dake karamar hukumar Kala balge na jahar Borno.

Daraktan watsa labaru na rundunar Sojan sama, Ibikunle Daramola ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, 7 ga watan Feburairu a babban birnin tarayya Abuja, inda yace rundunar ta samu wannan nasara ne ta hannun dakarunta dake yaki a fagen fama a karkashin Operation Lafiya Dole.

Daramola yace Sojoji sun kai wannan hari ne a ranar 5 ga watan Feburairu bayan samun bayanan sirri game da ayyukan mayakan ISWAP wadanda suka tare a sansanonin bayan sun taso daga Tongue.

A cewarsa, rahotanni sun bayyana cewa mayakan ISWAP sun taso daga Tongue sun kafa sansanoni a Kaza tare da makamansu da kuma kayan abincinsu da sauran kayan amfaninsu na yau da kullum.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel