Dalilin da yasa ba zan iya sa baki cikin lamarin Ganduje da Sarkin Kano ba - Buhari

Dalilin da yasa ba zan iya sa baki cikin lamarin Ganduje da Sarkin Kano ba - Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Juma'a ya bayyana cewa ba zai iya sanya baki cikin rikicin masarautar Kano da gwamnatin jihar ba saboda majalisa ta riga da sa baki.

Buhari ya bayyana hakan ne yayinda ya karbi bakuncin gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje da wasu manyan jigogin APC a fadar shugaban kasa, Aso Villa Abuja.

"Bisa ga kudin tsarin mulkin Najeriya, gwamnan jihar Kano na da nasa hurumin, muddin lamari ya shiga hannun yan majalisa (misali lamarin Kano), shugaban kasa bai da hakkin sa baki," Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya nakalto daga Buhari.

Legit Hausa ta kawo muku rahoton yadda gwamnan jihar Kano ta majalisar dokokin jihar ya kirkiro sabbin masarautu hudu.

Alkaluma sun bayyana cewa gwamnan ya yi hakan ne domin rage karfin sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu wanda yayi adawa da gwamnan a zaben 2019.

Hakazalika gwamnan ya yi barazanar kwancewa sarkin rawani bisa zargin rashin biyayya.

Daga baya wasu manyan Arewa suka sanya baki domin sulhuntasu kuma suka hana gwamnan sauke sarkin.

Bayan ganawar da Ganduje yayi yau da Buhari, ya bayyanawa manema labarai cewa ana cigaba da zaman sulhu.

Dalilin da yasa ba zan iya sa baki cikin lamarin Ganduje da Sarkin Kano ba - Buhari
Dalilin da yasa ba zan iya sa baki cikin lamarin Ganduje da Sarkin Kano ba - Buhari
Asali: Twitter

Mun kawo muku rahoton cewa gwamnatin jihar Kano ta nisanta kanta daga sabuwar shirin tsaron da matasan Arewa suka kafa mai suna 'Shege-ka-fasa'.

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya bayyana hakan ne ranar Juma'a yayinda yake hira da manema labaran fadar shugaban kasa bayan ganawar jigogin APC na Kano da shugaba Muhammadu Buhari.

Ganduje ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta zuba kudade wajen tabbatar da tsaro a dukkan sassan jihar kuma basu bukatar wata kungiyar tsaro.

Hakazalika Sarkin musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar a ranar Alhamis ya ce sakacin 'yan bokon arewa ne yasa wasu matasan yankin suka kirkiri wata rundunar tsaro da suke kira 'Operation Shege Ka Fasa.'

Ya bukaci shugabanin yankin na Arewa su ja kunnen matasan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel