Taskar Kannywood: Gwamnatin Ganduje ta bude ma Sani Danja kamfaninsa da ta garkame

Taskar Kannywood: Gwamnatin Ganduje ta bude ma Sani Danja kamfaninsa da ta garkame

Babban sakataren hukumar tace fina finai na jahar Kano, Alhjai Ismai’ila Na’Abba Afakallahu ya bayyana cewa gwamnatin jahar Kano ta bude kamfanin daukan hotuna na Sani Danja da ta garkame a kwanakin baya.

Daily Trust ta ruwaito Afakallau ya bayyana haka ne a ranar Juma’a bayan gwamnati ta bude kamfanin kwanaki biyu da rufe shi sakamakon rashin bin ka’idoji wajen yi ma kamfanin nasa rajista.

KU KARANTA: Kwana 1 bayan Buhari ya rantsar da jiragen yaki, dakarun Sojin sama sun ragargaji Boko Haram

Sai dai Afakallau ya musanta rahotanni dake nuna cewa gwamnati ta garkame kamfanin ne tun da farko saboda siyasa, saboda a cewarsa sun rufe kamfanoni fiye da 20 tare da na Sani Danja sakamakon suna aiki ba bisa ka’ida ba.

Afakalallu yace Sani Danja ya kai shekaru biyu yana gudanar da kamfanin nasa ba tare da mallakar takardun da ake bukata wajen bude kamfani ba, sa’annan sun aika masa takardar gayyata domin sanar dashi matsayin da kamfaninsa yake ciki, amma ya ki amsawa, har sai da suka rufe kamfanin.

Amma Afakallahu yace sun bude kamfanin a yanzu bayan Danja ya mallaki dukkanin takardun da ake bukata. Sai dai duk kokarin da majiyarmu ta yi na jin ta bakin Sani Danja game da lamarin ya ci tura sakamakon bai amsa sakon kar ta kwana da aka tura masa ba.

Idan ba’a manta ba, Danja ya zargi gwamnatin Ganduje ta hannun hukumar tace fina fina a jahar Kano ta rufe masa kamfanin da ya bude na daukan hotuna saboda siyasa, sai dai hukumar ta musanta wannan zargi, inda tace jarumin bai yi ma kamfaninsa rajista ba.

Tun ba yau ba, Sani Danja ya yi suna wajen goyon bayan jam’iyyar PDP da kuma tsohon gwamnan jahar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, don haka baya tare da jam’iyyar APC da Gwamna Ganduje.

Danja ya ce, "Babu wata maganar yin rijista, akwai da ma mutanen da ake hakonsu saboda dalilai na siyasa. Kuma ni ina gaya wa mutane cewa su rika ganewa bambancin siyasa alheri ne; idan kana abu wanda babu wanda zai kalubalance ka abubuwa ba za su tafi daidai ba."

Sani Danja ya tabbatar da cewa ya yi rijista da dukkan hukumomin da ke kula da harkokin kasuwanci kafin kamfanin daukar hoton ya fara aiki, daga ciki har da hukumar rijstar harkokin kasuwanci ta Najeriya, Corporate Affairs Commissioin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng