Kayi zamanka amma Nagode - Gwamna Zulum ga matashin da ya alanta tattaki daga Jigawa zuwa Maiduguri

Kayi zamanka amma Nagode - Gwamna Zulum ga matashin da ya alanta tattaki daga Jigawa zuwa Maiduguri

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya yi kira ga matashi, Usman Zubairu, wanda ya sanar da cewa zai yi tattaki daga Jigawa zuwa Maiduguri domin jinjinawa gwamnan kan ayyukan da yake yi yayi zamansa amma ya gode.

Gwamnan ya bayyana hakan ne da yammacin Juma'a a shafinsa na Tuwita.

Yace: "A'a, Nagode, dan uwa Usman Zubairu."

"Na samu wani labarin cewa wani matashin 'dan uwa, Usman Zubairu, ya kaddamar da tattaki daga Jigawa zuwa Maiduguri domin karramani."

"Ina mai matukar godiya Malam Usman bisa ga goyon bayarka amma ina rokonka ya ajiye wannan tafiya."

"A nawa fahimtar, ya zo Maiduguri tuni. Ina kira garemu mu sanya jihar Borno da Najeriya cikin addu'o'inmu. Hakan ya fi kyau."

Usman Zubairu ya bayyana cewa zai yi tattaki daga jiharsa ta Jigawa zuwa Maiduguri domin nuna goyon baya ga gwamna Zulum kan namijin kokarin da yakeyi ga al'ummarsa.

Za ku tuna cewa A ranar Laraba ne Sarkin Rano, Alhaji Tafida Ila ya nada Nasiru Aliyu Batsari a matsayin Sarkin Zumuncin Rano.

Nasiru Aliyu Batsari dai ya yi tattaki ne a kasa tun daga Katsina har zuwa jihar Kano don nuna goyon bayansa ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Idan zamu tuna, Nura Aliyu Batsari mai shekaru 33 dan asalin karamar hukumar Batsari ne da ya taka a kasa tun daga jihar Katsina zuwa Kano. Tafiya ce mai nisan kilomita 172 a titi, don nuna farin cikinsa a kan nasarar da Ganduje ya samu a kotun koli.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel