Kwana 1 bayan Buhari ya rantsar da jiragen yaki, dakarun Sojin sama sun ragargaji Boko Haram

Kwana 1 bayan Buhari ya rantsar da jiragen yaki, dakarun Sojin sama sun ragargaji Boko Haram

Dakarun rundunar Sojan saman Najeriya sun tashi wasu sansanonin mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram, bangaren ISWAP a kauyen Kaza, dake karamar hukumar Kala balge na jahar Borno.

Daraktan watsa labaru na rundunar Sojan sama, Ibikunle Daramola ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, 7 ga watan Feburairu a babban birnin tarayya Abuja, inda yace rundunar ta samu wannan nasara ne ta hannun dakarunta dake yaki a fagen fama a karkashin Operation Lafiya Dole.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari za ta fara sayar da gidaje 1,094 da ta gina a jahohi 35

Kwana 1 bayan Buhari ya rantsar da jiragen yaki, dakarun Sojin sama sun ragargaji Boko Haram
Kwana 1 bayan Buhari ya rantsar da jiragen yaki, dakarun Sojin sama sun ragargaji Boko Haram
Asali: Facebook

Daramola yace Sojoji sun kai wannan hari ne a ranar 5 ga watan Feburairu bayan samun bayanan sirri game da ayyukan mayakan ISWAP wadanda suka tare a sansanonin bayan sun taso daga Tongue.

A cewarsa, rahotanni sun bayyana cewa mayakan ISWAP sun taso daga Tongue sun kafa sansanoni a Kaza tare da makamansu da kuma kayan abincinsu da sauran kayan amfaninsu na yau da kullum.

“Mun kai hare haren ne bayan mun gano sansanonin tare da dimbin yan ta’adda dake zaune a cikinsu, hakan ya haifar da tashin sansanonin gaba daya, tare da halaka mayakan ISWAP da dama.” Kamar yadda kamfanin dillancin labarun Najeriya ta ruwaito shi.

Daga karshe, Daramola yace rundunar Sojan sama tare da taimakon rundunar Sojan kasa zasu cigaba da aiki kafada da kafada domin kawo karshe yakin da suke yi da yan ta’adda a yankin Arewa maso gabas.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da wasu sababbin jiragen yaki guda 3 mallakin rundunar Sojan sama a kokarin da gwamnatinsa ta ke yin a shawo kan matsalolin tsaro da suka yi ma Najeriya katutu.

Buhari ya kaddamar da jiragen ne a ranar Alhamis, 6 ga watan Feburairu, inda ya rantsar da wasu jirage guda biyu kirar Agusta 109P helicopter da wani guda daya samfurin Mi0171E helicopter.

A jawabinsa, shugaba Buhari yace gwamnatin tarayya a karkashin shugabancinsa za ta yi duk mai yiwuwa don ganin ta magance matsalolin tsaron da suka addabi yan Najeriya, don haka yace gwamnatinsa ba za ta baiwa yan Najeriya kunya ba

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel