Kwalba ta buga mini a kai ni kuma na kasheta - Cewar saurayin da ya kashe budurwarshi a Bauchi

Kwalba ta buga mini a kai ni kuma na kasheta - Cewar saurayin da ya kashe budurwarshi a Bauchi

- Solomon Peter, saurayi mai shekaru 23 da ya kashe budurwarshi a jihar Bauchi ya ce kare kanshi yayi amma ba da niyya ba

- A ranar 24 ga watan Janairu ne Solomon ya kashe budurwarshi ta hanyar sukarta da wuka sakamakon amsa wayar wani namiji da tayi a gaban shi

- Ya ce yana da niyyar aurenta kuma yayi da ya sanin abinda ya aikata duk da ba da niyya yayi hakan ba

Solomon Peter mai shekaru 23 da ya kashe budurwarshi mai shekaru 25 ya ce ya kasheta ne yayin kare kan shi.

Idan zamu tuna, 'yan sanda sun kama Peter ne bayan mutuwar budurwarshi a ranar 24 ga watan Janairu sakamakon sukarta da yayi da wuka a baya.

A yayin tattaunawa da jaridar Daily Trust a ranar Laraba, wanda ake zargin ya ce ya soketa da wuka ne don kare kanshi bayan fadan da suka fara a kan amsa wayar wani gardi da yake zargin saurayinta ne kuma suna cin amanarshi.

"Muna shawo kan wata matasala ne. Wani mutum ya kira ta da karuwa. Sai na tambayeta me ke tsakaninsu har da zai yi hakan. Daga nan kawai sai ta fasa kwalba a kaina kuma akwai shaidun da suka ga abinda ya faru."

Ya ce bayan ta fasa kwalbar a kanshi ne ya shiga daki ya dauko wuka wacce ya soketa da ita, lamarin da yayi sanadin mutuwarta.

"Ban yi niyyar kasheta ba, na so kare kaina ne saboda kwalbar da ta fasa a kaina. Nayi aiki cikin fushi ne a kanta duk da kuwa aurenta nake son yi. Nayi dana-sanin abinda nayi duk da ba da niyya bane," ya kara da cewa.

KU KARANTA: Tashin hankali: Alade ya sha giya kwalba shida ya bugu yaje ya tsokano Sa sun dambatu

Wani makwabcin marigayiyar wanda ya bukaci a boye sunanshi ya sanar da jaridar Daily Trust cewa, duk yankin an san irin soyayyar da ke tsakaninsu. "Marigayiyar ta daga wayar wani abokinta namiji ne a gaban Solomon. Daga nan kishi ya tashi sai aka fara fada. Za ta yi bayani ne ya fara dukanta," in ji majiyar.

"Ta fasa kwalba wacce tayi amfani da ita wajen kare kanta saboda tsanantar dukan da yake mata. Tuni ya dauko wuka ya soke ta a baya, lamarin da ya ja ta rasa jini mai tarin yawa. Da safe an kaita asibiti kuma an dawo da ita gida. Da yamnaci ne jikinta yayi zafi inda aka mayar da ita asibitin kafin ta ce ga garinku."

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Bauchi, DSP Kamal Abubakar ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Ya ce, "a lokacin da ya ga ta zubar da jini sosai, sai ya kaita asibiti. Sun dubata ba tare da sanar da 'yan sanda. A don haka ne muka kama mai asibitin tare da ma'aikatanshi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel