Yanzu-yanzu: Ganduje, 'yan majalisa da sarakuna sun kai wa Buhari ziyara (Hotuna)

Yanzu-yanzu: Ganduje, 'yan majalisa da sarakuna sun kai wa Buhari ziyara (Hotuna)

Shugaba Muhammadu Buhari ya na ganawa da wata tawagar 'yan siyasa da shugabanni al'umma daga Kano da suka kai masa ziyara a fadar Aso Rock karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Daily Trust ta ruwaito cewa shugaban masu rinjaye na Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa; Sanata Kabiru Gaya suna daga cikin 'yan Majalisar Tarayya da Sarakuna da ke cikin tawagar.

Kawo yanzu dai ba a san takamamen dalilin da yasa gwamnan da tawagarsa suka kai wa shugaban kasar ziyarar ba.

DUBA WANNAN: Yadda 'yan sanda suka kama 'yan uwansu 'yan sanda da ke karbar cin hanci a Legas (Bidiyo)

A wani rahoton kun ji cewa Sarkin Ningi na jihar Bauchi, Alhaji Yunusa Danyaya, ya roki shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan ya ceto masarautar Kano daga wargajewa da gaggauwa. Ya roki shugaban kasan ya saka baki a kan barakar da ke tsakanin Sarkin kano, Alhaji Muhammadu Sanusi II da kuma Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, Basaraken ya yi wannan rokon a ranar Alhamis ne yayin tattauna da manema labarai a fadarsa da ke garin Ningi. Ya ce kiran ya zama dole ne idan aka dubi yadda wutar baraka ke ruruwa tsakanin sansui da Ganduje.

"Ina rokon shugaban kasa a matsayin uba ga kowa da ya duba girman Allah ya shiga cikin matsalar da ke tunkarar Kano kuma ya sasanta tsakanin Sarki da Gwamna. Ina da tabbacin cewa Buhari ba zai bar masarautar Kano ta tabarbare ba kuma a tozarta ta," ya yi kira.

Basaraken ya ce Buhari ya kasance mutum mai matukar girmama masarautun gargajiya. Ya kara da cewa: "Wannan ya zama dole mu kai kokenmu wajen mahaifinmu, uban kasarmu, Shugaban kasa Muhammadu Buhari. Zai iya shawo mana kan matsalarmu saboda ya shawo kan matsalar da ta fi wannan a baya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel