Mai yayi zafi: Miji ya kashe matarsa ya binne gawarta a cikin dakinsu

Mai yayi zafi: Miji ya kashe matarsa ya binne gawarta a cikin dakinsu

- Rundunar 'yan sandan jihar Bayelsa ta cafke Monday Uwem mai shekaru 30 sakamakon zargin shi da ake da kashe matar shi

- Monday ya kashe Blessing Menaboo ne mai shekaru 26 sannan ya haka karamin kabari a madafinsu inda ya birneta

- Makwabtansu ne suka garzaya wajen 'yan sanda don sanar musu da abinda ke faruwa wanda hakan yayi sanadin kamen

Rundunar 'yan sandan jihar Bayelsa ta cafke Monday Uwem mai shekaru 30 sakamakon zargin shi da ake da halaka matar shi Blessing Menaboo mai shekaru 26.

Jaridar Within Nigeria ta gano cewa wanda ake zargin ya birne gawar matar shi din a madafin gidansu da ke sansanin kamun kifi na Aparama da ke yankin Akassa a karamar hukumar Brass ta jihar Bayelsa.

Kamar yadda rahotanni suka nuna, an kama wanda ake zargin ne bayan makwabtan shi sun fallasa abinda ya faru.

A yayin martani kan mummunan al'amarin, kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Butswat Asinim ya tabbatar da kamen wanda ake zargin mai suna Uwem.

KU KARANTA: Tsananin sanyi ya sanya yanzu bama samun kasuwa - Karuwan jihar Kano sun koka

"An fara binciken yadda aka kashe wata mata mai suna Blessing Menaboo mai shekaru 26. Tana zama ne a sansanin kamun kifi da ke Akassa a karamar hukumar Brass ta jihar Bayelsa.

"An zargi mijinta mai suna Monday Uwem ne da kasheta tare da haka kabari a madafinsu inda ya birneta.

"An kama wanda ake zargin tare garkame shi bayan ya amsa laifin shi. Za a ci gaba da gabatar da bincike." Ya ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel