An kama 'yar sanda da ta yi ta murde mazakutar wani makanike a caji ofis

An kama 'yar sanda da ta yi ta murde mazakutar wani makanike a caji ofis

Rundunar 'yan sandan jihar Rivers ta kama wata mata da ake zargin cewa ta matse mazakutar wani makanike, Ikwunado Chima a lokacin da ake gana masa azaba a caji ofis bayan 'yan sanda sun kama shi.

Marigayi Chima ya rasu ne a hannun 'yan sandan a ranar 23 ga watan Disamban 2019 kwanaki hudu bayan da aka kama shi kamar yadda The Punch ta ruwaito.

An gano cewa an kama 'yar sandan da aka ce sunan ta Rose a ranar Laraba tare da wasu 'yan sandan shida da ake zargin suna da hannu a mutuwar Chima yayin da ya ke tsare a hannun hukuma.

An kama 'yar sandan da ta 'yamutsa' mazakutar wani makanike
An kama 'yar sandan da ta 'yamutsa' mazakutar wani makanike
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yadda miji ya kashe matarsa suna tsakiyar saduwa saboda fushin tana haihuwa barkatai

Tawagar 'yan sanda ta Eagle Crack ne suka kama Chima da abokansa hudu a hanyarsu ta zuwa gida a cikin motarsu a kan zargin cewa 'yan fashi ne su.

Duk da cewa mai motar ya shaidawa 'yan sandan cewa Chima da abokansa ba su aikata ko wanne laifi ba, 'yan sandan sun cigaba da gana musu azaba har sai da makaniken ya mutu a hannun 'yan sandan.

Bayan sakinsu, abokan Chima sun ce Rose ta shigo dakin da ake gana musu azaba ta yi ta damkar mazakutar Chima tana barazanar cewa za ta ga bayansu.

"Ta shigo ne a lokacin da ake azabtar da Chima kuma ta rika damkar mazakutarsa. Ina tausaya wa mijin irin wannan matar."

Majiyar ta ce kwamandan Eagle Crack, Adetuyi Benson ta riga ya mika 'yan sandan hudu zuwa sashin binciken manyan laifuka na 'yan sanda CIID inda aka tsare su kafin a kamo 'yar sandan.

Sai dai mai magana da yawun 'yan sandan jihar, Mista Nnamdi Omoni ya ce ba a sanar da shi batun kama 'yar sandan ba, ya ce ya san cewa ana gudanar da bincike a kan 'yan sanda hudu da suka kama makaniken da abokansa hudu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel