An samu maganin Coronavirus, an sallami mutane 1,153 daga asibiti
An sallami mutane 1,153 da suka kamu da cutar Coronavirus daga asibiti bayan an tabbatar da warkewansu a ranar Laraba, 5 ga watan Febrairu 2020, jami'an kiwon lafiyan kasar Sin sun laburta.
A ranar Laraba kadai, mutane 261 sun koma gidajensu daga Asbiti, rahoton kullum na hukumar kiwon lafiya kasar ya bayyana.
Mun kawo muku rahoton cewa a jiya Laraba, Akalla mutane 490 sun mutu kawo yanzu a sakamakon cutar coronavirus da ta barke a kasar Sin. Wannan cuta ta fito ne a Yankin Wuhan, kafin cutar ta fara zagaya Duniya.

Asali: Twitter
Kawo yanzu akwai mutane 24,500 da su ka kamu da wannan cuta a fadin Duniya. Ga jerin kasashe 28 da cutar ta bulla yanzu:
1. Sin - 20,438
2. Australiya - 14
3. Belguim - 1
4. Cambodia - 1
5. Canada - 4
6. Finland - 1
7. Faransa - 6
8. Jamus - 12
9. Hong Kong - 21
10. Indiya - 3
11. Italy - 2
12. Japan - 33
13. Macau - 10
14. Malaysiya - 12
15. Nepal - 1
16. Phillipines - 3
17. Rasha - 2
18. Singapore - 28
19. Koriya ta kudu - 19
20. Spain - 1
21. Sri Lanka - 1
22. Sweden - 1
23. Taiwan - 11
24. Vietman - 10
25. Thailand - 25
26. UAE (Dubai) - 5
27. Birtaniya - 2
28. Amurka - 11
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng