Hukumar INEC za ta kirkiro sabbin rumfunan zabe kafin zaben gama gari na 2023

Hukumar INEC za ta kirkiro sabbin rumfunan zabe kafin zaben gama gari na 2023

Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta bayyana cewa tana duba yiwuwar kirkiro sabbin rumfunan zabe domin ta kara adadinsu kafin babban zaben gama gari na shekarar 2023 ta yadda masu zabe zasu samu saukin kada kuri’unsu kamar yadda doka ta tanada.

Shugaban hukumar INEC, Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Alhamis, 6 ga watan Feburairu ta hannun daraktan watsa labaru da wayar da kan masu zabe, Oluwole Osaze-Uzzi.

KU KARANTA: Buhari ya rantsar da wasu sabbin jiragen yaki 3 na rundunar Sojan sama

Hukumar INEC za ta kirkiro sabbin rumfunan zabe kafin zaben gama gari na 2023
Hukumar INEC za ta kirkiro sabbin rumfunan zabe kafin zaben gama gari na 2023
Asali: Facebook

Sanarwa ta ce shugaban INEC ya bayyana haka ne yayin da ya samu bayanan taswirar kasa, GIS, daga hukumar tallafa ma harkokin zabe na kungiyar nahiyar kasashen Turai, a ranar Laraba, a babban birnin tarayya Abuja.

Yakubu yace “A yanzu haka Najeriya tana da rumfunan zabe 119,973, rumfunan zabe na biyu akalla 57,000, amma idan ka duba taswirar kasar, zaka gane cewa inda babu rumfunan zabe sun fi yawa a kan masu rumfunan zabe. Don haka GIS zai taimaka mana wajen aiwatar da wannan aiki.”

Ya kara da cewa: “Wannan gudunmuwa da kuka bamu ba zai tafi ga banza ba, zai kara mana himma kwarai da gaske wajen shirye shiryen zaben 2023, musamman wajen kirkiro sabbin rumfunan zabe. Najeriya kasa ce mai yawan jama’a, kuma karuwa adadin jama’a yake, a duk lokacin da na yi tafiya sai naga wani sabon yanki ya kafu.”

Daga karshe Yakubu ya kara da cewa a yanzu haka INEC tana aiki tare da hukumar kidaya ta kasa don samar da sabbin rumfunan zabe.

A wani labarin kuma, INEC ta kashe jam’iyyun Najeriya guda 73 saboda a cewarta sun gaza wajen cika ka’idojin zama jam’iyyun siyasa, sa’annan ta bar jam’iyyu guda 18 wanda ta bayyanasu a matsayin tsayayyun jam’iyyun siyasa a Najeriya.

Shugaban INEC, Mahmud ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labaru a ranar Alhamis, inda yace akwai jam’iyya daya da ta zamo musu karfe kafa, APP, sakamakon ta garzaya gaban kotu, kuma kotu ta nemi INEC ta saurara har sai ta yanke hukunci, don haka APP na cikin tsayayyun jam’iyyu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: