Buhari ya rantsar da wasu sabbin jiragen yaki 3 na rundunar Sojan sama
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da wasu sababbin jiragen yaki guda 3 mallakin rundunar Sojan sama a kokarin da gwamnatinsa ta ke yin a shawo kan matsalolin tsaro da suka yi ma Najeriya katutu.
Punch ta ruwaito Buhari ya kaddamar da jiragen ne a ranar Alhamis, 6 ga watan Feburairu, inda ya rantsar da wasu jirage guda biyu kirar Agusta 109P helicopter da wani guda daya samfurin Mi0171E helicopter.
KU KARANTA: Akwai yiwuwar gwamnatocin kasashen waje na tallafa ma Boko Haram – Majalisa

Asali: UGC
A jawabinsa, shugaba Buhari yace gwamnatin tarayya a karkashin shugabancinsa za ta yi duk mai yiwuwa don ganin ta magance matsalolin tsaron da suka addabi yan Najeriya, don haka yace gwamnatinsa ba za ta baiwa yan Najeriya kunya ba.
Haka zalika a jawabin nasa, shugaba Buhari ya nanata manufar gwamnatinsa na karkatar da alakar tattalin arzikin Najeriya daga man fetir domin samun karin kudaden shiga don gudanar da aikace aikacen daya sanya a gaba.

Asali: UGC
“Mun kudiri aniyar daukan duk matakan da suka kamata don cimma sakamakon da muke bukata, sayan wadannan jirage na daga cikin kokarin da muka yi, sa’annan mun sayi wasu makamai da dama don baiwa Sojojinmu kwarin gwiwa, duk da kalubalen da muke fuskanta na kasafin kudi.
“Don haka zamu cigaba da yin iya kokarinmu don tabbatar da kowanne bangare na kasar nan ya shaida ikirarin da muke yi na kawo canjin da muka yi alkawarin zamu kawo a kasar.
“Kimanin shekara daya da ya gabata ma na rantsar da wasu jirage 2 kirar Agust a rundunar Sojan sama, jiragen nan zasu taimaka ma dakarun sojan sama wajen fuskantar kalubalen da muke fuskanta a kasarmu a yau.” Inji shi.

Asali: UGC
A wani labarin kuma, Manyan hafsoshin tsaron kasa sun bayyana ma majalisar wakilai cewa akwai hannun kasashen waje a cigaba da ruruwar matsalolin tsaro a Najeriya, musamman matsalar ta’addanci da sauran kalubalen tsaro.
Manyan hafsoshin tsaron sun bayyana haka ne yayin wata ganawar sirri da suka yi da kwamitin tsaro ta majalisar wakilai, kamar yadda shugaban kwamitin, Babajimi Benson ya bayyana ma manema labaru.
Babajimi yace hafsoshin tsaron sun yi bayanai da dama game da tsaro, don haka akwai bukatar zama a tattaunasu daya bayan daya, muhimmi daga ciki shi ne akwai yiwuwar sa hannu daga kasashen waje a rikicin.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng