Shari'ar mutumin da ya hada bidiyon 'auren' Buhari ta samu cikas

Shari'ar mutumin da ya hada bidiyon 'auren' Buhari ta samu cikas

Hukumar tsaro ta fararen kaya, ta gurfanar da Muhammad Kabir, wani mutum da aka kama shi bisa zargin hadawa da yada bidiyon shagalin bikin Shugaba Muhammadu Buhari da ministar agaji, jin kai da inganta jama'a, Sadiya Umar Farouq.

An samu matsala a kotun Majistare din ne da ke Kano a ranar Laraba yayin da aka gurfanar da shi don fara sauraron tuhumar da ake masa. Kafin fara shari'ar, sai mai gabatar da kara, Iliya Bulus ya ce yana neman a ba shi lokaci tukunnan, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Ya sanar da kotun cewa akwai bukatar ya aika wa Antoni Janar kuma kwamishinan shari'ar jihar da fayil din binciken Kabiru, don ya bada shawarar da ta dace.

Bulus ya ce a bangarensu, suna yin duk abinda ya dace don ganin sun nemi shawarwari daga kwamishinan shari'ar jihar.

Shari'ar mutumin da ya hada bidiyon 'auren' Buhari ta samu cikas
Shari'ar mutumin da ya hada bidiyon 'auren' Buhari ta samu cikas
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Shari'ar Zazkzaky: An tsananta tsaro a Kaduna

Ali Jamilu, lauyan Kabiru bai yi ja-in-ja ba kan dage shari'ar da kotun za ta yi. Sai dai kuma ya roki kotun da ta sassauta sharadin belin da aka gindaya wa Kabiru. Sharadin belin kuwa shi ne Kabiru zai dinga kai kansa ofishin DSS na Kano a kowacce rana.

Mai shari'ar ya amshi wannan rokon kuma tare da amincewa. Ya umarci Kabiru da ya dinga kai kansa ofishin DSS din sau daya a kowanne mako

Daga nan ne aka dage sauraron karar zuwa ranar 24 ga watan Maris, domin ba wa kwamishinan shari'ar jihar Kano damar samun isasshen lokacin da zai yi nazarin fayil din tuhumar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel