Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: Saurayi ya yiwa uwarshi da ubanshi yankan rago

Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: Saurayi ya yiwa uwarshi da ubanshi yankan rago

- Jamia’an ‘yan sandan sashin bincike na musamman a kan kisan kai na jihar Legas na neman wani saurayi mai shekaru 23

- Ana zargin saurayin ne da kashe mahaifin shi da mahaifiyar shi ta hanyar soka musu waka

- Kafin wanda ake zargin ya gudu, ya samu kanwarshi wacce ya soka wa wuka a ciki da hannu amma ba ta mutu ba

Jami’an ‘yan sanda na runduna ta musamman a kan binciken laifukan kisa a jihar Legas sun bazama neman wani matashi mai shekaru 23.

An zargi Michael Okhide da sokawa mahaifinshi mai suna Barista Clement Okhide wuka tare da mahaifiyar shi wanda hakan yayi sanadin mutuwarsu har lahira.

An gano cewa matashin ya soka wa kanwar shi wuka a ciki da hannu kafin ya tsere, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Mummunan lamarin ya faru ne a ranar Talata, 4 ga watan Fabrairu 2020 a gida mai lamba 6 titin Akeen Gbadamosi da ke Ejigbo, a jihar Legas.

KU KARANTA: Boko Haram na gab da ganin bayan mu baki daya - Mutanen garin Chibok

An gano cewa, wanda ake zargin ya ajiye gawar mahaifin nashi a madafi ne yayin da ya kulle gawar mahaifiyar shi a wani daki a cikin gidan kafin ya gudu.

Wata majiya daga jami’an tsaron ta ce sunan mahaifiyar wanda ake zargin Toyin Okhide kuma tana da shekaru 50 ne a duniya.

Majiyar daga ‘yan sandan ta ce wanda ake zargin ya soki kanwar shi a ciki da kuma hannu kafin ya gudu. “Kanwar ta shi da ta samu raunikan na asibitin Ejigbo inda take samun taimakon likitoci. Gawar iyayenshi kuwa tana nan a ma’adanar gawawwaki da ke asibitin.”

Majiyar ta ce jami’an tsaron na ta kokarin ganin sun kama wanda ake zargin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel