Kokarin juya shari'ar kotun koli: Ihedioha ya dauki lauyoyi 30

Kokarin juya shari'ar kotun koli: Ihedioha ya dauki lauyoyi 30

Makonni uku bayan kotun kolin Najeriya ta kwace kujerar Emeka Ihedioha na gwamnan jihar Imo, ya koma kotun domin ganin yadda za'a iya juya shari'ar.

Yayinda yake hira da manema labarai a Abuja, Ihedioha ya ce ya shigar da kara jiya inda ya bukaci kotun soke shari'ar da ta yanke da farko.

Ya ce tuni ya dauki lauyoyi 30 karkashin jagorancin tsohon Antoni Janar, Kanu Agabi, domin su wakilesa a kotun kolin.

Wanda yayi jawabi a madadin Ihedioha, tsohon kwamishanan shari'ar jihar Imo, Ndukwe Nnawuchi, ya bayyanawa manema labarai cewa sun kyautata zaton samun nasara.

Yace: " A ranar Laraba, Emeka Ihedioha da jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sun dauki lauyoyi domin sake duba shari'ar kotun koli. Lauyoyin sun duba kuma suna baiwa Ihedioha shawarar matakin da zai dauka."

"Bisa shawararsu, Ihedioha da PDP sun umurci lauyoyin su garzaya kotun koli domin shigar da karar yadda za'a soke shari'ar da aka yanke ranar 14 ga Junairu, 2020."

"Ina mai sanar da ku cewa (jiya), lauyoyin sun shigar da kara."

KU KARANTA: Mutum 3 sun hallaka, 179 sun jikkata yayinda jirgin saman yayi kaca-kaca a Turkiyya

Mun kawo muku rahoton Kotun kolin ta alanta Hope Uzodinma na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) matsayin zakaran zaben gwamnan 9 ga Maris, 2019.

Dukkan Alkalan kotun kolin sun yi ittifaki a shari'ar da Mai shari'a Kudirat Kekere-Ekun ta karanto cewa an zagbewa jam'iyyar APC kuri'un rumfunan zabe 388 yayinda ake tattara sakamakon zaben jihar Imo.

Mai shari'a Kudirat Kekere Ekun tace bayan an hada kuri'un runfuna 388 da aka zabge a farko da kuri'un da yan takaran suka sami, dan takarar APC ya kamata ace hukumar INEC ta sanar matsayin zakaran zaben.

Saboda haka, ta yi watsi da sanarwan INEC na baiwa Emeka Ihedioha nasara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel