Akwai yiwuwar gwamnatocin kasashen waje na tallafa ma Boko Haram – Majalisa

Akwai yiwuwar gwamnatocin kasashen waje na tallafa ma Boko Haram – Majalisa

Akwai yiwuwar wasu gwamnatocin kasashen waje suna baiwa kungiyar yan ta’addan Boko Haram makudan kudade a matsayin tallafin ta’addanci da suke aikatawa a Najeriya, inji dan majalisa Babajimin Benson.

Benson wanda shi ne shugaban kwmaitin tsaro na majalisar ya bayyana haka ne a ranar Laraba bayan wata ganawar sirri da ya yi da manyan hafsoshin tsaro na Najeriya wanda ya gudana a majalisar wakilan Najeriya.

KU KARANTA: Yan matan Chibok su 100 sun yi bore a jami’ar Atiku Abubakar dake jahar Adamawa

A makon da ta gabata ne biyo bayan hauhawar matsalolin tsaro a kasar, shi ne majalisar wakilai ta yi kira ga manyan hafsoshin tsaro dasu yi murabus, idan kuma ba haka ba shugaban kasa ya tsige su.

Sai dai daga bisani majalisar ta yanke shawarar gayyatar manyan hafsoshin tsaron, inda garkame kofa suna goga gemu da gemu na tsawon lokaci tare da mambobin kwamitin tsaro.

Da yake zantawa da manema labaru bayan kammala ganawar, Mista Benson yace: “Akwai kamshin gaskiya a rahotannin da ake samu na cewa wasu manyan kasashen duniya suna da hannu cikin yakin ta’addancin da ake samu a Najeriya”

Sai dai Benson bai bude ma yan jaridu cikinsa sosai ba, amma dai ya kwatanta alakar ISIS da ISWAP, inda yace wadannan batutuwa ne dake bukatar tattaunawa ta musamman.

“Abin da muke so yan Najeriya su sani shi ne a shirye muke don ganin mun hada hannu da Sojoji domin kawo karshen matsalar nan cikin dan lokaci. Mun gamu da bayanan da suka bamu, kuma zamu mika shawarwarinsu gaban majalisa don ganin yadda zamu taimaka.” Inji shi.

Da yake ganawa da manema labaru kafin fara zaman kwamitin, kaakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila ya bayyana cewa makasudin gayyatar manyan hafsoshin tsaron shi ne don jin ta yaya yan Najeriya ke mutuwa kamar babu tsaro a kasar.

“Mun san dai manyan matsalolinsu basa wuce rashin kayan aiki, karancin ma’aikata da sauransu wanda zasu bayyana mana idan an shiga ganawar sirrin, amma muna da tabbacin kwamitinmu zasu iya kula da wannan matsalar.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel