Yadda miji ya kashe matarsa suna tsakiyar saduwa saboda fushin tana haihuwa barkatai

Yadda miji ya kashe matarsa suna tsakiyar saduwa saboda fushin tana haihuwa barkatai

Wani mutum a kasar Brazil ya amsa cewa ya kashe matarsa ne a yayin da suke tsakiyar saduwa saboda fushin cewa ta sake samun juna biyu karo na uku.

Marcelo Araujo dan shekara 21 ya shaidawa 'yan sanda a Sao Paulo bayan an shafe makonni shida ana masa tambayoyi cewa ya kashe matarsa mai sana'ar yi wa mutane kwaliya, Francine dos Santos, mai shekaru 22 bayan sunyi musayar kalamai kan juna biyun da ta sake dauka karo na uku.

Ya bayyana cewa baya son karin haihuwa saboda ya ki jinin yadda hankalin matar ke rabuwa tsakaninsa da yaran kuma yana matukar damuwa saboda kudin da ya ke kashewa domin kulawa da yaran.

Yadda miji ya kashe matarsa suna tsakiyar saduwa saboda fushin tana haihuwa barkatai
Yadda miji ya kashe matarsa suna tsakiyar saduwa saboda fushin tana haihuwa barkatai
Asali: Twitter

Ma'uaratan suna da yara biyu, mace mai shekaru hudu da na miji dan shekara biyu.

DUBA WANNAN: Ganduje da Sanusi: Sarkin Ningi ya bawa Buhari shawara

Da ya ke bayar da ba'asi kan yadda rikicinsu ya samo asali, Mista Araujo ya yi ikirarin cewa a watan Decemban 2019, sun fara tattauna yadda za su yi bikin Kirsimeti amma sai suka fara musayar kalamai a kan juna biyun da ta ke dauke da shi.

Yadda miji ya kashe matarsa suna tsakiyar saduwa saboda fushin tana haihuwa barkatai
Yadda miji ya kashe matarsa suna tsakiyar saduwa saboda fushin tana haihuwa barkatai
Asali: Twitter

Jim kadan bayan sun kammala musayar kalaman, sun huce fushinsu kuma suka nufi daki domin suyi kwanciya irin ta masoya. A yayin da suke tsakiyar saduwa ne wanda ake zargin ya yi amfani da wuka ya yi ta caka wa matarsa kuma daga bisani ya yanke ta a wuya.

Bayan ya aikata laifin, ya yi yunkurin ya kashe kansa.

Yan sanda sun tsinci shi da munanan rauni a wuyansa da hannunsa a gidansu da ke Varzea Paulista da ke jihar Sao Paulo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel