Babbar magana: Mijina na kwanciya da makwabcinmu suna luwadi tare - Matar aure ta fasa kwai

Babbar magana: Mijina na kwanciya da makwabcinmu suna luwadi tare - Matar aure ta fasa kwai

- Wata mata ta bada labarin yadda mijinta ke luwadi da makwabcinta inda daga baya ya koma kan yaron da yake mata aiki a gida

-Yaron da ke musu aikin gida ya gudu amma da ta same shi sai ya sanar da ita yadda mijinta ke sa shi ya dinga shigar shi ta baya

- Makwabciyarta kuwa ta sanar da ita cewa ta ga mazansu na sumbatar juna amma ita tana tsoron tunkarar mijinta don yana dukanta

Wani kwararren mai bayar da shawara kuma masani a fannin zamantakewa, Joro Olumofin ya bada labarin wata mata da mijinta ke lalata da maza. Ya dade yana luwadi da makwabcinshi kuma yana lalata yaron gidansu mai musu aiki, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Matar ta bayyana yadda take tsananin son mijinta kuma ta kasa rabuwa da shi. Labarinta kuwa ya jawo cece-kuce daga ma’abota amfani da kafar sada zumuntar zamani.

Ga cikakken labarinta:

“A boye sunana. Jiya nayi gwajin cutar kanjamau da cutukan da ake iya diba ta wajen saduwa. Mijina ne yake luwadi da makwabcinmu. Yadda asirin shi ya fara tonuwa kuwa shine a shekarar da ta gabata sai yaron da ke mana aiki ya gudu. Yaron yana da shekaru 19 amma aji shida yake na firamare. Da ya gudun kuwa bai satar min komai ba. Hakan sai yayi matukar bani mamaki don kuwa na ga kayan karau dina da kudina.

“Na je gidan iyayenshi amma sai da suka nemi yi min duka tare da jifa na da duwatsu. Na shiga matukar mamaki don ban san dalili ba. Da na koma gida sai na sanarwa mijina amma sai ya ce kila suna da tabin kwakwalwa ne.

KU KARANTA: Labari mai dadi: Amurka ta bawa Najeriya tallafin dala miliyan 40 don yaki da ta'addanci

“Daga baya sai naje makarantarsu yaron don hankalina bai kwanta ba. Daga nan ne ya fara kuka tare da sanar dani yadda mijina ke tilasta shi yin lalata dashi ta baya. Mijina na saka mishi basilin a mazakutar shi sai ya ce ya dinga shigar shi ta baya. Na shiga tasin hankali don har hatsari na kusa yi a hanyar komawa gida.

“Na dade ina ganin jini a karamin wandon mijina amma idan na tambayeshi sai ya ce sikari ne ke mishi illa. A wannan shekarar kuwa sai makwabciyata ta sanar da ni cewa ta ga mijinta da nawa na sumbatar juna. Ita bata san abin yi ba saboda tana tsoron mijinta don yana dukanta. Gaskiya ina son mijina kuma ina son in ci gaba da zama da shi don mutumin arziki ne. Me ya dace inyi?”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel