Sokoto: Tambuwal zai gina katafaren filin wasanni da ya kai girman na Olympic

Sokoto: Tambuwal zai gina katafaren filin wasanni da ya kai girman na Olympic

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya ce yana shirin gina wani katafaren filin wasanni mai girmar irin wanda ake amfani da shi a wasannin kasashen duniya (Olympic) a babban birnin jihar domin inganta cigaban wasanni.

Mai magana da yawun gwamnan, Muhammad Bello, ya ce Tambuwal ya yi wannan jawabin ne a ranar Laraba lokacin da ya kai ziyarar bazata wurin da ake ginin filin wasanni na tunawa da Giginya a Sokoto da ake shirin gudanar da wasannin kwallon hannu na kasa na 'yan kasa da shekaru 12 da 15.

Gwamnan ya jadada aniyar gwamnatinsa na ganin ta samar da yanayin mai kyau da ya dace domin cigaban wasanni a jihar, "domin ganin ta dawo martabar ta da aka san ta da shi a fanin wasanni a duniya."

Sokoto: Tambuwal zai gina katafaren filin wasanni da ya girman na Olympic
Sokoto: Tambuwal zai gina katafaren filin wasanni da ya girman na Olympic
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Jerin kasashe 10 da gwamnati ke rokar 'yan kasa a kan su kara haihuwa

A cewarsa, jihar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wurin ganin ta samar wa maza da mata kayayyakin wasanni na zamani domin su samu damar nuna bajinta da suke da shi.

Ya bayyana gamsuwarsa kan yadda aikin ginin ke tafiya kuma ya umurci ma'aikatar cigaban matasa da wasanni na jihar ta samar wa 'yan kwangilar wasu kudade da za su taimaka wurin ganin an samar da wasu kayayyakin aiki a filin wasan.

Da ya ke zagawa da gwamnan yayin da ya ziyarci cibiyar wasannin, direktan da ke kula da aikin ginin, Masallem Engineering Nigeria Limited, Abuja, Danjuma Musa, ya ce ana kan ginin filayen wasannin kwallon hannu, kwallon kwandom, kwallon kafa da sauransu.

Ya kuma ce za a samar a dakin canja kaya na 'yan wasa, da na masu horar da 'yan wasa da dakin ajiyar kayayakin kallo.

Mista Masu ya tabbatar wa gwamnan cewa an dauki matakan tsaro da suka dace don ganin kayayyakin filin wasan ba su lalace ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel