Shege-Ka-Fasa: Arewa za ta kafa rundunar tsaronta na musamman (Hotuna)

Shege-Ka-Fasa: Arewa za ta kafa rundunar tsaronta na musamman (Hotuna)

Hadakan kungiyoyin Arewa (CNG) ta sanar da kafa rundunar tsaro na yankin da ta yi wa lakabi da "Shege-Ka-Fasa".

Wannan na zuwa ne kimanin wata guda bayan gwamnonin yankin Kudu maso yamma sun kafa rundunar tsaro makamancin wannan da suka saka wa suna Amotekun kamar yadda The Cable ta ruwaito.

A yayin taron manema labarai a ranar Labara, mai magana da yawun kungiyar, CNG ta ce ta rubuta wasika domin neman goyon baya daga kungiyar gwamnonin jihohin arewa (NSGF).

Ya ce idan gwamnonin arewa da shugabanin yankin ba su bayar da hadin kai da ake bukata ba, CNG za ta nemi izinin kafa rundunar daga wurin hukumomin tarayya da abin ya shafa.

Abdulazeez ya ce, "An kafa rundunar ne domin samar da tsaro a yankin arewa ba tare da nuna banbancin kabila ko addini ba kuma za su kasance masu kishin kasa wurin gudanar da ayyukansu na tallafawa wurin samar da tsaro a yankin."

Ga wasu daga cikin hotunan dakarun rundunar da motocinsu a kasa:

Kungiyar Arewa ta kafa rundunar tsaro - kamar Amotekun (Hotuna)
Motar rundunar tsaro ta Shege Ka Fasa na Arewa
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Jerin kasashen duniya 10 da gwamnati ke rokar 'yan kasa a kan su kara haihuwa

Kungiyar Arewa ta kafa rundunar tsaro - kamar Amotekun (Hotuna)
Dakarun tsaro na Kungiyar Shege Ka Fasa
Asali: Twitter

Kungiyar Arewa ta kafa rundunar tsaro - kamar Amotekun (Hotuna)
Hotunan Dakarun kungiyar Arewa ta Shege Ka Fasa
Asali: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel