Buhari ya fi kula da yan Boko Haram fiye iyalan wadanda suka kashe

Buhari ya fi kula da yan Boko Haram fiye iyalan wadanda suka kashe

Kungiyar Kiristocin Najeriya CAN ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ta fi mayar da hankali wajen kula da yan Boko Haram fiye iyalan wadanda ya ta'addan suka cutar.

CAN ta bayyana hakan ne a martanin da ta mayarwa shugaba Buhari kan jawabinsa na cewa kashi 90 na wadanda Boko Haram ke cutarwa Musulmai ne.

Kungiyar Kiristocin Najeriya CAN ta fusata da maganar shugaba Muhammadu Buhari cewa kashi 90 na wadanda Boko Haram ke kashewa Musulmai ne.

Kungiyar ta bayyana cewa wannan jawabi ya nuna karara gwamnatin Buhari na siyasantar da rayukan mutane.

Diraktan yada labaran kungiyar, Kwamkur Samuel, a hirar da yayi da Punch, yace:

"Kungiyar Kiristocin Najeriya na bayyana bacin ranta kan jawabin karya, mara asali da hujja, da shugaba Buhari yayi na cewa kashi 90 na wadanda Boko Haram ke kashewa Musulmai ne.

"Karanta irin wannan jawabin ban haushin daga shugaban kasa, ko shakka babu Buhari bai fahimci ainihin wadanda ake kashewa ba dubi ga irin hare-haren da ake kaiwa Kiristoci."

Buhari ya fi kula da yan Boko Haram fiye iyalan wadanda suka kashe
Buhari ya fi kula da yan Boko Haram fiye iyalan wadanda suka kashe
Asali: Facebook

A jiya, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce kashi 90 na wadanda Boko Haram ke kashewa Musulmai ne sabanin rade-radin da wasu kungiyoyi ke cewa Kirista ake kashewa.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan a jawabin da saki a mujjalar Kirista 'Christianity Today'.

Buhari yace: "Har yanzu bamu samu nasarar yakan karya da gaskiya ba. Addinin Kirista a Najeriya ba kamar yadda wasu ke tunani bane na kamar ana cin zalin mabiyanta, kulli yaumin karuwa addinin take kuma yawan mabiyanta ya kusa rabin adadin yan Najeriya."

"Hakazalika maganar cewa mabiya addinin Kirista yan Boko Haram sun kaiwa hari; ba dukkan yan matan Chibok ne Kirista ba, wasunsu Musulmai ne, kuma dukkansu yan ta'adda suka sace."

"Maganar gaskiya da ake gani zahiri itace kashi 90% na wadanda Boko Haram ke kaiwa hari Musulmai ne: wannan ya hada da sace dalibai mata Musulmai 100, harbe-harbe cikin Masallaci; da kisan shahrarrun Limamai biyu."

"Abinda kowa ya sani shine wadannan yan ta'addan suna kaiwa marasa galihu hari, masu addini, marasa addini, yara, da manya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel