Sana’a sa’a: Gwamnati na neman matasa masu sana’ar hannu domin fara aiki a kasar Jamus

Sana’a sa’a: Gwamnati na neman matasa masu sana’ar hannu domin fara aiki a kasar Jamus

Gwamnatin kasar Jamus tana neman yan Najeriya matasa masu sana’o’in hannu domin su koma kasar Jamus da zama tare da amfani da damarmaki birjik na aikace aikace dake kasar, kamar yadda wata babbar jami’ar gwamnatin kasar ta bayyana.

Jami’ar, mai suna Annette Widmann-Mauz, wanda karamar minista ce a gwamnatin kasar Jamus kuma kwamishiniyar hijira tare da kula da walwalar yan gudun hijira ta bayyana haka ne a ranar Laraba yayin ziyarar da ta kai ziyara zuwa ofishin kwamishinan kula da yan gudun hijira na Najerita, Sanata Bashir Muhammad Lado.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Annobar zazzabin Lassa ta kashe mutane 2 a jahar Katsina

Sana’a sa’a: Gwamnati na neman matasa masu sana’ar hannu domin fara aiki a kasar Jamus
Ziyarar
Asali: Facebook

A jawabinta, Annette ta ce: “Nahiyar Afirka na da matukar muhimmanci ga Jamus da siyasa da tattalin arzikin nahiyar Turai, a yan kwanakin ma mun samar da sabbin dokokin zama a kasarmu wanda ya bamu daman neman matasa masu sana’o’in hannu daga wajen nahiyar Turai.

“Najeriya kasa ce mai tarin matasa majiya karfi, kuma akwai yiwuwar samun likitoci, injiniyoyi da sauran kwararru daga cikinsu, don haka muke neman hanyoyin sanar dasu yadda zasu iya komawa kasar Jamus. Amma ko da yake a yanzu haka akwai matasanku da yawa dake zuwa Jamus ba ta hanyoyin da suka kamata ba.

“Don haka nake sanar daku cewa a yanzu muna neman kwararru ne kawai.Za mu kafa cibiyoyi a sassan kasar domin fahimtar da yan Najeriya hanyoyin daya dace su bi wajen samun shiga Jamus tare da tarewa da zama a can.” Inji ta.

A nasa jawabin, kwamishinan tarayya mai kula da yan gudun hijira, Sanata Bashir Lado ya yi maraba da wannan tsari, inda yace tuni Najeriya ta shiga cikin sabon tsarin da duniya ta yadda da shi na shiga da fice a kasashe, kuma zasu cigaba da sanya idanu tare da auna matsayin gudanar da tsare tsaren.

A wani labarin kuma, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa akwai shirin daukan sabbin zaratan Sojoji nan bada jimawa ba a kokarin gwamnatin Najeriya na kara adadin jami’an tsaro domin su kawar da matsalar tsaro a kasar.

Osinbajo ya bayyana haka ne a ranar Litinin, 3 ga watan Feburairu yayin da ya karbi bakoncin wasu Fastoci a karkashin kungiyar fastocin yankin Arewacin Najeriya masu rajin kawo zaman lafiya a yankin.

Osinbajo ya bayyana cewa: “Muna yin duk mai yiwuwa don ganin an kawo karshen matsalar tsaro, muna tafiyar da tsaron nan yadda ya kamata, daga ciki har da aika Sojoji bakin daga domin yaki da Boko Haram a yankin Arewa maso gabas."

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel