Tirkashi: An nada tsohuwa mai shekaru 118 a matsayin mai bada shawara ta musamman

Tirkashi: An nada tsohuwa mai shekaru 118 a matsayin mai bada shawara ta musamman

Brian Wotari, mataimakin shugaban karamar hukumar Kolokuma/Opokuma a jihar Bayelsa ya nada Omonigbalebo Dani Orogono mai shekaru 118 a matsayin mai bada shawar ta musamman a kan lamurran dattijai.

An bayyana nada Orogono ne a wata wasika mai kwanan wata 4 ga watan Fabrairu, 2020 kuma ta samu saka hannun Bedford Ineye, daya daga cikin hadiman mataimakain shugaban karamar hukumar.

“Da matukar farin ciki nake sanar da nada ki mai bayar da shawara ta musamman a kan lamurran dattijai ga mataimakin shugaban karamar hukumar Kolokuma/Opokuma.

“Tun daga yau wannan nadin ya fara aiki. Ina taya ki murna tare da miko gaisuwar mataimakin shugaban karamar hukuma.”

Tirkashi: An nada tsohuwa mai shekaru 118 a matsayin mai bada shawara ta musamman
Tirkashi: An nada tsohuwa mai shekaru 118 a matsayin mai bada shawara ta musamman
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Kurunkus: Nathaniel Samuel ya fadi sunan wacce ta tura shi cikin coci da bam

Ebinimi Abiama, wani mazaunin yankin, ya sanar da jaridar The Cable cewa wannan nadin ya biyo bayan kara da aka yi ga dattijan yankin.

“Ba wai an nada ta bane don bada shawarar za a ce,” ya ce.

“Amma wannan nadin anyi ne don dattijan yankin su san ana tafiyar tare da su. Nadin karramawa ne. Itace ta fi kowa tsufa a karamar hukumar. Albashin da za a dinga biyanta kuwa don ta samu na amfani da shi ne, ” ya kara da cewa.

Kamar yadda ya ce, “Mataimakin shugaban karamar hukumar yayi haka ne don tallafawa tare da daga yanayin rayuwata. Ya gyara mata gidanta kafin nan.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel