NYSC: Saurayi da budurwa da ke hidimar kasa a Kano zasu yi aure

NYSC: Saurayi da budurwa da ke hidimar kasa a Kano zasu yi aure

Wasu masu hidimar kasa a jihar kano, Mohammed Alhaji Musa da Hauwa Yahaya Bagudu zasu yi aure a ranar Juma'a mai zuwa.

Shugaban NYSC na jihar Kano, Malam Ladan Baba ya sanar da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a ranar Laraba cewa wasu daga cikin 'yan bautar kasa na kashin farko na shekarar 2019 sun sanar da shi cewa zasu yi aure.

Kamar yadda shugaban hukumar ya sanar, a lokacin da dan asalin jihar Nasara din da 'yar jihar Neja suka same shi a kan zasu yi aure, sai ya ce su samu iyayensu don samun yardarsu.

"Na ce su samu iyayensu don yarjewa. Daga nan sai su samu NYSC din yadda zamu shiga ciki. Tun daga nan ban kara ji daga wajensu ba har sai kusan makonni shida da suka gabata da suka kawo min katin gayyata. Ina matukar farin ciki." ya ce.

DUBA WANNAN: Dan takarar neman zama kwamanda a Hisbah ya shigar da karar hukumar a Kano

Baba yayi bayanin cewa aurensu ne na farko a jihar wanda za a yi tsakanin 'yan bautar kasa daga jihohi daban-daban. Hakan kuwa ya bayyana kadan daga cikin amfanin bautar kasar na hada 'yan sassa daban na kasar nan.

A yayin bayanin yadda suka hadu da amaryarsa, Alhaji ya ce sun fara haduwa ne a madafi yayin da suke sanasanin 'yan bautar kasan.

Daga nan ne ya je har gidan iyayenta don bayyana niyyarsa. Ya ce ya ji dadin yadda aka karbeshi hannu bibbiyu.

"Da farko yanayin rayuwarta ne ya ja hankali na, saukin kanta da yadda ta ke mutunta mutane, wanda na lura da shi a zaman mu na sansanin. Daga nan na fara son ta.

"Da farko ban so zama in yi hidimar kasa a Kano ba don Abuja na so. Amma kuma daga baya sai na hakura don kuwa alheri ne ya kaini da kuma rabo," ya ce.

A bangaren Banufiya Hauwa daga jihar Neja, ta ce ta amince da auren Alhaji Musa ne sakamakon halayensa na gari da ta lura da su tun a sansanin 'yan bautar kasan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel