Jerin kasashe 10 da gwamnati ke rokar 'yan kasa a kan su kara haihuwa

Jerin kasashe 10 da gwamnati ke rokar 'yan kasa a kan su kara haihuwa

Sakamakon halin da duniya ta ke ciki na rayuwa, akwai kasashen da basu amincewa 'yan kasarsu a kan su yi ta haihuwa . Kasashen kan kayyadewa jama'ar kasar iya yawan yaran da suke bukata.

Amma kuma abin mamaki shine akwai kasashen duniya da ke kara wa 'yan kasar karfin guiwar haihuwa. Su kan shawarci 'yan kasar da su haifa ko ba don kasnu ba toh don gwamnatin kasar. Ga kadan daga cikin wadannan kasashen a duniya:

1. Denmark

Kasar Denmark na kira ga 'yan kasar a kan cewa koda ba zasu haifa 'ya'ya don kansu ba, toh su haifa don kasar Denmark.

Matan karamar kasar ba su haihuwa akai-akai. Akwai wani kamfani da ke bada hasafi ga mata a don karfafa musu guiwa kan su kara haihuwa.

2. Russia

Kasar Rasha na daya daga cikin kasashen da ke ba wa mata karfin guiwa kan su kara haihuwa. Kasar na fama da mutuwar maza sakamakon cutar HIV da kuma shan giya.

Wannan matsalar ta yawaita ne a 2007 ne lokacin da kasar Rasha ta fitar da ranar 12 ga watan Satumba don daukar ciki.

A ranar ne ma'aikata ke hutun aiki don su mayar da hankali wajen yin ciki don haihuwa. Matan da suka haihu bayan watanni tara cif ana basu kyautar firij.

3. Japan

Yawan haihuwa a kasar Japan ya kara kamari ne tun a shekarar 1975. Kasar na karfafa guiwar maza a kan su yi wa matansu ciki don haihuwa ko don su samu yawan jama'ar kasar ya karu.

4. Romania

A shekarar 1960 ne kasar Romania ta ke roko tare da yi wa wadanda zasu yi aure gata. Rashin haihuwar yayi yawa ta yadda aka fara cin harajin ma'auratan da basu da 'ya'ya. Sun kafa dokokin da suka hana sakin aure kwata-kwata

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Dan sanda ya kashe kansa a Legas

5. Singapore

A ranar 9 ga watan Augusta na 2012 ne gwamnatin kasar Singapore ta yi wani taron dare a kasar wanda ke karfafa guiwar 'yan kasar a kan su haihu.

Kasar ta kafa doka a kan yawan mutane masu zama a daki daya don a samu a dinga yin ciki tare da haihuwa. A kowacce shekara gwamnatin kasar na kashe a kalla $1.6 biliyan don shirin da 'yan kasar zasu kwanta da juna har su haihu.

6. South Korea

A kowacce ranar Laraba ta mako na uku a wata, kasar tana kashe wutar ofisoshi da karfe 7 na yamma. Ana kiran ranar da ranar iyali.

Gwamnatin kasar na bada kudi a matsayin kyautatta ga jama';arta don su haihu.

7. India

Duk da yawan kasar Indiya, yawan haihuwa ba matsala bane a kasar don kuwa har nemanta ake. Akwai shirye-shirye da ke bada karfin guiwar saduwa da iyali ba tare da anyi amfani da kwararon roba ba.

Hakazalika ana karfafa ma mazan guiwa a kan su hanzarta barin gidan iyayensu don su fara tara iyalinsu.

8. Italy

Duk da ci gaba da kasar ta ke wajen kira da jawo hankulan jama'arta a kan su haihu, har yanzu dai ba wani yawan a zo a gani suke da shi ba.

Mutane da yawa na ganin cewa kiran da suke yi sam bai samu nasara ba don kuwa har yanzu ba yawa gare su ba

9. Hong Kong

Hong Kong na fuskantar babbar matsala ta yadda mutane ke tsufa amma babu matasa da ke shirye don maye gurbinsu. Hakan kuma yana jawo lalacewar tattalin arzikin kasar kamar yadda suka bayyana.

10. Spain

Rashin haihuwa a kasar Spain kullum karuwa yake sannan kuma rashin aikin yi na karuwa. A kalla rabin matasan kasar basu da aikin yi. Sannan kuma ba a ci gaba da haihuwa a kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel