Yanzu-yanzu: Trump ya sha da kyar, Majalisa ba ta kama shi da laifi ba

Yanzu-yanzu: Trump ya sha da kyar, Majalisa ba ta kama shi da laifi ba

- Yunkurin da 'yan jam'iyyar Democrats su kayi na tsige Shugaba Donald Trump bai cimma nasara ba

- Majalisar Dattijai a ranar Laraba, 5 ga watan Fabrairu ta wanke Trump daga da zargin aikata laifuka biyu da aka gabatarwa

- Tunda an kawo karshen shari'ar, Trump zai cigaba da kasancewa shugaban Amurka kuma zai iya neman takara domin zarcewa karo na biyu

Majalisar Dattijai a ranar Laraba, 5 ga watan Fabrairu ta wanke Trump daga da zargin aikata laifuka laifuka da neman tsige shi da aka gabatar da gabata.

CNN ta ruwaito cewa an wanke Trump daga zargin aikata laifukan biyu da suka hada da amfani da ofishinsa ba ta hanyar da ta dace ba da kuma yi wa majalisar kasar katsalandan.

Legit.ng ta gano sanatocin sun wanke Trump ne bayan jefa kuri'u 52-48 a kan zargin amfani da karfin ikonsa ba ta hanyar da ta dace ba yayin da suka jefa 53-47 a kan zargin yi wa majalisa katsalandan.

Yanzu-yanzu: Trump ya sha da kyar, Majalisa ba ta kama shi da laifi ba
Yanzu-yanzu: Trump ya sha da kyar, Majalisa ba ta kama shi da laifi ba
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Dan sanda ya kashe kansa a Legas

Tunda an kammala shari'ar a majalisar, Shugaba Trump zai cigaba da kasancewa shugaban Amurka kuma yana da daman sake neman zarcewa karo na biyu.

A martanin da ya yi a baya, Trump ya ce tsigewar da majalisar wakilai suka yi masa ba shi ake hari ba sai dai mutanen Amurka.

Trump ya bayyana yunkurin tsige shi a matsayin juyin mulki da 'yan Democrats suka nemi yi masa.

Majalisar Wakilai ta Amurka ta tsige Trump ne a cikin watan Disamban 2019.

An zarge shi ne da amfani da karfin ofishinsa wurin yi wa kasar Ukraine matsin lamba ta sanar da fara bincike a kan abokin hamyyarsa gabanin babban zaben da za a gudanar a wannan shekarar da kuma yin katsalandan cikin ayyukan majalisa.

Shugaba Trump ya yi ta nanata wa cewa shi bai aikata wani laifi ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel