Yanzu-yanzu: Jirgin sama ya rabe biyu yayinda ya sauka, mutane 177 ke ciki

Yanzu-yanzu: Jirgin sama ya rabe biyu yayinda ya sauka, mutane 177 ke ciki

Wani jirgin saman kasar Turkiyya dauke da fasinjoji 177 ya sauka daga kan titi yayinda ya sauka a filin jirgin saman Istanbul kuma ta rabe biyu a ranar Laraba, 5 ga watan Junairu, 2020, amma jami'ai sun bayyana cewa babu wanda ya mutu.

Jirgin ya taso ne daga birnin Izmir domin zuwa filin jirgin saman Sabiha Gokcen kuma yanayin sararin samaniya babu kyau.

Dan jaridan NTV ya nuna hotuna dake nuna jirgin ta kama da wuta amma daga baya jami'an kwana-kwana suka kashe wutan.

Hotunan a kasar Turkiyya sun nuna yadda fasinjoji ke fitowa daga cikin jirgin ta inda ta rabe biyu.

Yanzu-yanzu: Jirgin sama ta rabe biyu yayinda ta sauka, mutane 177 ke ciki
Yanzu-yanzu: Jirgin sama ta rabe biyu yayinda ta sauka, mutane 177 ke ciki
Asali: Facebook

Ministan Sufuri Mehmet Cahit Turhan yace babu wanda ya mutu, kuma yawancin fasinjojin sun sauka fita daga cikin jirgin da kansu.

"Wasu fasinjoji sun fita daga jirgin da kansu yayinda wasu ke turke ciki kuma ma'aikatanmu na kokarin fito da su." Yace

Gwamnan jihar Ali Yerlikaya yace: "A yanzu, mutane 120 suka jikkata kuma an kaisu asibiti... dukkansu na nan lafiya illa mutum daya zuwa biyu."

Allah ya kiyaye "da abin ya fi haka."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel