Dan takarar neman zama kwamanda a Hisbah ya shigar da karar hukumar a Kano

Dan takarar neman zama kwamanda a Hisbah ya shigar da karar hukumar a Kano

Wani jami'in hukumar Hisbah mai suna Bashir Ja'afar ya shigar da karar hukumar reshen jihar Kano a gaban hukumar karbar korafe-korafe ta Kano (Anti Corruption).

Bashir Ja'afar ya zargi hukumar Hisbah din da tauye masa hakkinsa a yayin jarabawar sabbin kwamandojin ta na kananan hukumomi.

Hukumar ta kafa kwamitin tantancewa ne da jarabawa ga kwamandojin kananan hukumomi karkashin tsohon babban kwamandan hukumar, Malam Ibrahim Mu'azzam Maibushra.

Bayan tantancewar ne Bashir Ja'afar ya samu maki 81 da digo shida amma sai Abdulrazak Imam ya samu maki 66 da digo 12 cikin dari.

Amma sai hukumar Hisbah suka sanya Abdulrazak Imam a matsayin kwamanda shi kuma Bashir Ja'afar aka ce ya karbi mataimaki.

Dan takarar neman zama kwamanda a Hisbah ya shigar da karar hukumar a Kano
Dan takarar neman zama kwamanda a Hisbah ya shigar da karar hukumar a Kano
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Tsaro: Hotunan sabbin jiragen yaki da kasar Rasha ta kera wa Najeriya

Wakilin gidan rediyon Freedom ya samu zantawa da Dakta Aliyu Musa Kibiya wanda shi ake zargi da wannan sauyi. Shugaban ya shaida cewa Bashir Ja'afar baya ckin 'yan takarar kwamandojin kananan hukumomin.

Don haka za a iya cewa kukan dadi yake yi.

Shugaban hukumar karbar korafe-korafen ta jihar Kano, Muhyi Magaji Rimin Gado ya ce sun karba koken kuma zasu gayyaci hukumar Hisbah din domin fadada bincike.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel