Kotu ta yanke hukunci kan matar da ta shiga Masallaci da kare

Kotu ta yanke hukunci kan matar da ta shiga Masallaci da kare

A ranar Laraba ne alkali ya wanke tare fitar da wata mata Kirista wacce ta shiga masallaci da kare tare da takalmanta. Kamar yadda alkalin ya ce, matar bata da cikakken hankali ne.

Matar mai suna Suzethe Margaret mai shekaru 52, an kama ta ne bayan ta shiga wani masallaci a kusa da Jakarta a watan Yuni 2019. Ta ce tana neman mijinta ne wanda ta sakankance yana cikin masallacin za a daura masa aure, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Wannan abin da tayi kuwa ya bata wa Musulmai rai, wadanda suke ganin kare a matsayin dabba mara tsarki kuma suna cire takalmi kafin su shiga masallaci domin yin sallah.

Kotu ta yanke hukunci kan matar da ta shiga Masallaci da kare
Kotu ta yanke hukunci kan matar da ta shiga Masallaci da kare
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Dan sanda ya kashe kansa a Legas

Shugaban alkalan kotun yankin Cibinong da ke Jakarta ya ce an gano cewa Margaret na fama da wata cuta a kwakwalwarta.

Babban alkalin, Indra Vidi ya ce wacce ke kare kanta ba za a iya kama ta da laifin aikinta ba don haka kotu ta wanke ta.

Amma kuma dan sanda mai gabatar da kara ya bukaci a daureta na watanni takwas.

Bidiyon da matar ke ta ihu tare da hargagi a cikin masallaci ya watsu a kafar sada zumuntar zamani a 2019, lamarin da ya jawo cece-kuce daga masu kallo.

A cikin bidiyon an ji matar na kiran kanta da Kirista mai bin darikar Katolika.

Amma kuma rahoton 'yan sanda ya nuna cewa likitoci sun gano tana da matsalar kwakwalwa tun a 2013.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel