Abinda Abdulmumin Kofa ya fada bayan ya ziyarci Ganduje (Hotuna)

Abinda Abdulmumin Kofa ya fada bayan ya ziyarci Ganduje (Hotuna)

A jiya ne tsohon dan majalisar wakilai da ya sha kaye a zaben maye gurbi na jihar Kano ya kaiwa gwamna Abdullahi Umar Ganduje ziyara. Abdulmumin Jibrin Kofa ya ziyarci Ganduje ne duk da kuwa barakar da ake ta cewa tana tsakaninsu.

An zargi gwamna Ganduje da hada kai da shugaban jam'iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas wajen goyawa abokin adawar Kofa baya don lashe kujerar majalisar wakilai ta Kiru/Bebeji.

Abinda Abdulmumin Kofa ya fada bayan ya ziyarci Ganduje (Hotuna)
Abinda Abdulmumin Kofa ya fada bayan ya ziyarci Ganduje (Hotuna)
Asali: Twitter

A ziyarar daAbdulmumin Kofa ya kai wa Ganduje, ya sha alwashin zasu ci gaba da yi wa jam'iyya biyayya tare da kokarin habaka ta matakin jihar da ta tarayya.

Abinda Abdulmumin Kofa ya fada bayan ya ziyarci Ganduje (Hotuna)
Abinda Abdulmumin Kofa ya fada bayan ya ziyarci Ganduje (Hotuna)
Asali: Twitter

Bayan shan kasan da Kofa yayi a zaben maye gurbin da aka yi watan Janairu na wannan shekarar, an ga Ganduje tare da Aliyu Datti-yako, wanda ya maka Kofa da kasa.

DUBA WANNAN: Fitattun 'yan Najeriya 8 da ciwon 'kansa' ya hallaka (Hotuna)

A hotunan da suka bayyanan, an ga Aliyu Datti na nuna wa Gwamna Ganduje shahadarsa komawa majalisar wakilai, lamarin da ya jawo cece-kuce daga jama'a da dama.

Abinda Abdulmumin Kofa ya fada bayan ya ziyarci Ganduje (Hotuna)
Abinda Abdulmumin Kofa ya fada bayan ya ziyarci Ganduje (Hotuna)
Asali: Twitter

Bayan ganawar da tsohon dan majalisar wakilan suka yi da Ganduje, ya ce zasu ci gaba da goyon bayan gwamnan jihar Kano da jam'iyyar APC din a matakin jiha da ta tarayya.

Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na tuwita, "A yau Laraba ne na kaiwa Gwamna jihar Kano, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ziyara. Za mu ci gaba da goyon bayan gwamnan da jam'iyyar APC a matakin jihar da tarayya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel