Yanzu-yanzu: An gurfanar Hamisu Wadume da Kyaftin Balarabe a kotu

Yanzu-yanzu: An gurfanar Hamisu Wadume da Kyaftin Balarabe a kotu

Bayan watanni shida da damkeshi, an gurfanar da shahrarren mai garkuwa da mutane, Hamisu Bala Wadume, gaban kotu kuma an cajeshi da laifuka 16 wadanda suka hada da ta'addanci, kisan kai da garkuwa da mutane.

A cewar Punch, lauyoyin hedkwatar hukumar yan sanda a Abuja; Simon Lough, Anthony Egwu, da Peter Amadi ne suka gurfanar da shi.

An gurfanar da Wadume ne tare da Kyaftin na Soja, Tijjani Balarabe, wanda yayi sanadiyar kisan yan sanda 4 domin tsiratar da Wadume da wasu yan bindiga 18.

Laifin farko yace: "Kai Alhaji Hamisu Bala, aka, Wadume, Capt Ahmed Tijjani Balarabe, ASP Aondona Iorbee; Insp. Aliyu Dadje; Auwalu Bala; Uba Bala; Ahmad Suleiman; Bashir Waziri; Zubairu Abdullahi; Rayyanu Abdul da wasu abokanku da suka gudu, kun hada baki domin garkuwa da Usman Garba, aka, Mayo a gidan mansa dake Takum tsakanin watan Febrairu da Afrilu 2019."

"Lauyoyin hukumar yan sanda sun bayyana cewa sun shirya shaidu 29, wasu zasuyi shaida kan yadda Wadume da yaransa sukayi garkuwa da Usman Garba da aka sace ranar 16 ga Febraoru 2019 a Takum."

"Sun bukaci kudin fansan N200 million sannan suka kashi bayan karban N106.3m."

"Daga cikin shaidun akwai DCP Abba Kyari, CSP Baba Khali, ASP Abdulrahman Mohammed, ASP Bawa James, Insps Habila Samuel and Ilarju Joseph saboda su suka gudanar bincike kan lamarin kuma zasu gabatar da hujjoji."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel